Fitaccen Malamin Addini Ya Gargadi Tinubu Yayin da Aka Sace Shugaban PDP, Ya Hango Sabuwar Matsala

Fitaccen Malamin Addini Ya Gargadi Tinubu Yayin da Aka Sace Shugaban PDP, Ya Hango Sabuwar Matsala

  • Fitaccen malamin addini ya yi sabon hasashe da ke nuna bullar sabuwar kungiyar yan ta'adda, masu fashi da makami da garkuwa da mutane
  • Primate Elijah Ayodele ya gargadi Shugaban kasa Bola Tinubu da ya dauki matakin gaggawa kan rashin tsaro don ceto gwamnatinsa daga fuskantar matsin lamba
  • Ayodele ya yi gargadin ne a daidai lokacin da labarin sace shugabannin jam'iyyun adawa, ciki harda na PDP a jihar Legas ya bayyana

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

An gargadi Shugaban kasa Bola Tinubu kan sabuwar kungiyar masu garkuwa da mutane da ta kunno kai cikin kankanin lokaci, kuma cewa manyan mutane suke niyar farmaka.

Shugaban cocin INRI Evangelical Spiritual, Primate Elijah Ayodele, ne ya gargadi Tinubu a sabon hasashensa, rahoton Daily Independent.

Kara karanta wannan

"Matata ta mayar da hankali kan harkokin addini bata kula da ni", miji ya nemi a raba aurensu

Malamin addini ya gargadi Tinubu kan tsaro
Fitaccen Malamin Addini Ya Gargadi Tinubu Yayin da Aka Sace Shugaban PDP, Ya Hango Sabuwar Matsala Hoto: Bola Ahmed Tinubu, Nigeria Police Force
Asali: Twitter

Ya kuma bukaci shugaban kasar da ya mayar da hankali sosai wajen yakar rashin tsaro saboda ya hango wata sabuwar kungiya ta yan ta'adda, masu fashi da makami da garkuwa da mutane.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ayodele ya yi hasashen garkuwa da mutane zai je mataki na gaba

Jaridar Daily Independent ta rahoto cewa, malamin addinin ya yi gargadin ne a cikin wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin labarai, Osho Oluwatosin, ya fitar.

Sanarwar ta kuma bayyana cewa malamin addinin ya yi hasashen cewa za a yi garkuwa da manyan mutane a kasar.

Ya kara da cewar garkuwa da mutane zai yadu zuwa yankuna da dama na kasar, kuma gwamnatin Shugaba Tinubu za ta fuskanci matsin lamba.

Wani bangare na sanarwar na cewa:

"Shugaban kasar na bukatar daukar matsalar rashin tsaro da matsin tattalin arziki da muhimmanci sosai.

Kara karanta wannan

Tinubu zai mayar da babban birnin tarayyar Najeriya Legas? Sanata Shehu Sani

"Za a yi garkuwa da manyan mutane, kuma na hango sabuwar kungiya ta yan fashi da makami, yan ta'adda da masu garkuwa da mutane suna tasowa."

Yan bindiga sun sace shugaban PDP

A wani labarin, mun ji cewa miyagun da suka yi garkuwa da shugaban jam'iyyar PDP reshen jihar Legas, Philip Aivoji, sun aiko da saƙon buƙatar a biya kuɗin fansa.

Masu garkuwan sun buƙaci a tattaro musu Naira miliyan 200 a matsayin kuɗin fansa kafin sako babban ɗan siyasan, cewar rahoton The Nation.

Asali: Legit.ng

Online view pixel