Manyan Labarai A Yau
Jihohin Arewacin Najeriya da dama ka iya fuskantar matsalar ƙarancin ruwan sama a daminar bana ta wannan shekarar. Kaduna, Yobe na daga cikin jerin jihohin.
Rahotanni sun tabbatar da tashin wani abu da ake kyautata zaton bam ne a jihar Jigawa. Lamarin ya auku ne cikin babban birnin jihar wato Dutse a ranar Talata.
Dakarun sojoji sun kai sumame wasu gidajen karuwai da ke a birnin Maiduguri na jihar Borno. Sojojin sun kulle gidajen sannan suka tasa keyar wasu mutane a wurin
Rahotanni sun nuna cewa jita-jita ta yi ta yawo kan batun murabus din shugaban jam'iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Adamu. Jam'iyyar ta fito fili ta musanta hakan.
Wata tsohuwa mai safarar miyagun ƙwayoyi ta faɗa komar jami'an hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi (NDLEA) a jihar Rivers. An same ta kayan miliyoyi.
Rahotanni sun bayyana cewa an dakatar da shugaban kamfanin jirgin sama na Arik Air, daga shiga cikin harabar kamfanin. Jami'an tsaro sun bayar da dalilai..
Rahotanni sun nuna cewa zaɓaɓben gwamnan jihar Benue, Hyacinth Alia, yayi watsi da shirin gwamnan jihar, Samuel Ortom, na kafa wata sabuwar doka kan fanshon sa.
Rundunar NSCDC ta samu nasarar kama wasu manyan motoci guda biyu ɗauke da wasu duwatsu masu daraja a jihar Zamfara. Rundunar ta bayyana dalilin kama motocin.
Wani matashi ya gamu da ajalin sa bayan an cinna masa wuta a jihar Cross River. Ana zargin matashin ne da laifin satar wayar Android yayi ɓatan dabo da ita.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari