Manyan Labarai A Yau
Primate Elijah Ayodele ya bayyana matakin da kungiyar ECOWAS ta dauka na tura sojoji Nijar a matsayin matakin da bai dace ba, ya ce tattaunawa ita ce mafita.
Ƙungiyar likitoci masu neman ƙwarewa (NARD) ta sanar da janye yajin aikin da take yi a faɗin ƙasar nan kan buƙatun da take neman gwamnatin tarayya ta biya musu.
Jam'iyyar All Progressives Congress (APC) reshen jihar Kano ta sha alwashin kwato karin kujerun siyasa a kotun zabe, ciki harda kujerar gwamna Abba Kabir Yusuf.
Shugaban kasar Kwaddibuwa, Alasanne Ouattara, ya ayyana sojojin juyin mulkin jamhuriyar Nijar a matsayin 'yan ta'adda, waɗanda ya kamata a yaka. Ya bayyana.
Al'ummar garin Zaria ta jihar Kaduna sun shiga tashin hankali yayin da rufin babban masallacin garin ya ruguzo yayin da masallata ke tsaka da Sallar la'asar.
An tabbatar da cewa kowane sanata daga cikin sanatoci 109 na majalisar dattawa ya samu N2m a matsayin kuɗin hutu wanda ya fara a ranar Litinin har zuwa Satumba.
Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya bayyana a wani tsohon bidiyo cewa zai goyi bayan gwamnatin shugaba Bola Tinubu a matsayin mashawarci daga waje.
Kungiyar ECOWAS ta ce gwamnatin mulkin soja a Jamhuriyar Nijar ta tsare hambararren shugaban kasa Mohamed Bazoum da dansa a cikin wani yanayi na rashin imani.
Wani matashi da ke zama a Turai da biyan kusan to £2,000 a matsayin kudin haya duk wata ya baje kolin karamin gidansa. Mutane sun sha mamakin abun da yake biya.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari