Rahoto Ya Tabbatar Da Kudaden Da Aka Tura Wa Sanatoci a Matsayin Kudin Hutu

Rahoto Ya Tabbatar Da Kudaden Da Aka Tura Wa Sanatoci a Matsayin Kudin Hutu

  • Majalisar dattawa na ci gaba da shan sun suka biyo bayan katoɓarar da shugabanta ya yi kan batun kuɗin shaƙatawar sanatoci
  • Akpabio, a yayin zaman majalisar na ranar Litinin, 7 ga watan Agusta, ya yi suɓutar baki inda ya ce sanatocin za su samu kuɗi domin hutun su na sati bakwai
  • Wani sanata wanda ya nemi a sakaya sunansa ya bayyana cewa da shi da sauran sanatocin, kowannen su an tura musu N2m

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT, Abuja - Biyo bayan kalaman shugaban majalisar dattawa Godswill Akpabio kan batun kuɗin hutun sanatoci, an tabbatar da cewa kowane sanata ya samu N2m a matsayin kuɗin alawus na zirga-zirga a lokacin hutun har zuwa watan Satumba, lokacin da za su dawo.

Kamar yadda Premium Times ta rahoto, alawus ɗin 2m na zirga-zirga su ne kuɗin da Akpabio yake maganar za a tura wa kowannen su a yayin zaman majalisar na ranar Litinin, 7 ga watan Agusta.

Kara karanta wannan

Juyin Mulkin Nijar: ECOWAS Ta Yi Sabon Jawabi Kan Halin Da Bazoum Da Dansa Ke Ciki a Tsare

An bayyana kudin da aka tura wa sanatoci
Wani sanata ya bayyana kudin da sanatoci suka samu domin hutu Hoto: Godswill Obot Akpabio
Asali: Facebook

Da yake tabbatar da hakan, wani sanata wanda ya nemi a sakaya sunansa ya bayyana cewa an tura wa kowane sanata N2m bayan zaman majalisar na ranar Litinin.

An tattaro cewa dukkanin sanatocin guda 109 na majalisar dattawa, N2m aka tura wa kowanen su wanda hakan ya sanya kuɗin sun kai jimillar N218m.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A ɗaya ɓangaren kuma, har yanzu ba a tabbatar da cewa ko Akpabio da sauran shugabannin majalisar N2m suka samu a matsayin kuɗin alawus ɗin hutun ba.

A bisa tsarin albashin da hukumar RMAFC ta amince da shi, albashin shugabannin majalisa ya fi na sauran sanatoci.

Shugabannin majalisar su ne, shugaban masu rinjaye, mataimakin shugaban masu rinjaye, babban mai tsawatarwa da mataimakin mai tsawatsarwa

Sauran sun haɗa da shugaban marasa rinjaye, mataimakin shugaban marasa rinjaye, ƙaramin mai tsawatsarwa da mataimakin ƙaramin mai tsawatarwa.

Kara karanta wannan

Daga Karshe Gaskiya Ta Fito Kan Makudan Kudaden Da Sanatoci Suka Samu Domin Shakatawa Lokacin Hutu

Na wa ne albashin sanatoci da shugabannin majalisa?

A tsarin albashin da hukumar RMAFC ta amince da shi, sanata yana samun N2,026,400 sannan yana samun alawus na N202,240 a shekara.

Albashin shugaban majalisar dattawa a shekara ya kai N2,483,242 sannan yana samuk alawus na N248,424 a shekara.

A na shi ɓangaren, mataimakin shugaban majalisar dattawa yana samun albashin N2,309,166, da alawus N230,916.

An Bukaci Akpabio Ya Yi Murabus

A wani labarin kuma, wani ɗan rajin gwagwaaya da kare dimokuraɗiyya ya yi wa shugaban majalisar dattawa Godswill Akpabio, wankin babban bargo.

Yimi Frank ya buƙaci Akpabio ya yi gaggawar sauka daga shugabancin majalisar sabida abin da ya kira abun kunyar da ya yi na tura wa sanatoci kuɗi domin shaƙatawa a lokacin hutu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel