Tsohon Ginin Massallacin Fadar Zazzau Ya Afkawa Mutane Yayin Da Ake Sallah La'asar

Tsohon Ginin Massallacin Fadar Zazzau Ya Afkawa Mutane Yayin Da Ake Sallah La'asar

  • Ginin Masallacin fadar Zazzau ya ruguzowa mutane yayin da suke tsaka da sauke farali
  • Lamarin ya afku ana cikin sallar La'asar a ranar Juma'a, 11 ga watan Agusta
  • Majiya ta tabbatarwa Legit.ng cewa an rasa rayuka biyu, za kuma a yi jana'izarsu da karfe 8:30 na dare a Fadar sarkin Zazzau

Zaria, Jihar Kaduna - Rahotanni da muke samu daga garin Zaria ta jihar Kaduna shine cewa rufin babban masallacin masarautar zazzau ya ruguzo yayin da al'ummar Musulmi ke tsaka da Sallah.

Kamar yadda shafin Dokin Karfe TV ta rahoto, lamarin ya afku ne a ranar Juma'a, 11 ga watan Agusta yayin da masallata ke tsaka da Sallar la'asar.

Masallaci ya ruguzo kan mutane
Tsohon Ginin Massallacin Fadar Zazzau Ya Afkawa Mutane Yayin Da Ake Sallah Hoto: @Kabir_Dillalai and @NFTfrea73507492
Asali: Twitter

Wani mazaunin unguwar Kaura Zaria mai suna Dahiru Mohammed ya tabbatarwa Legit.ng faruwar al'amarin inda ya ce ginin ya rufta ne a yayin da aka yi raka'a biyu ana na uku.

Kara karanta wannan

Nadin Ministoci: Yadda Masu Rike da Madafan Iko Su ka yi wa El-Rufai Taron Dangi

Ya kuma ce mutane biyu ne suka rasa rayukansu sannan wasu da dama sun jikkata inda aka kwashe su zuwa asibiti.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ce:

"Abin ya faru ne yau lokacin da ake sallar la'asar
"An yi raka'a biyu ana na uku ginin ya rufta."
Biyu sun mutu yayin da da dama sun jikkata, an kai su asbiti.

Sarkin Zazzau ya yi martani

Da yake tabbatar da lamarin, Mai martaba sarkin Zazzau, Mallam Ahmed Nuhu Bamalli, ya ce masallata na sallar la'asar da misalin karfe 4:00 na yamma lokacin da lamarin ya faru.

Yayin da yake ta'aziyya ga iyalan mamatan, sarkin ya yi umurnin cewa mutane su ci gaba da sallah a wajen masallacin har zuwa lokacin da za a yi gyare-gyare.

Za a yi jana'izar mamatan da karfe 8:00 na dare

Sarkin ya kuma ba da umurnin cewa a tu jana'izar dukka mamatan a yau da karfe 8:30 na dare a fadar sarkin.

Kara karanta wannan

Juyin Mulkin Nijar: ECOWAS Ta Yi Sabon Jawabi Kan Halin Da Bazoum Da Dansa Ke Ciki a Tsare

Jama'a sun yi jaje a kan lamarin

Abdulhadi Umar ya yi martani:

"Allah ya jiqan wadanda suka rasusu Kuma wadda sukaji rau nuka Allah ya basu lafiya."

Nasir Suleiman Ibrahim ya ce:

"Inna lillahi wa inna ilaihi raajiuun, Allah madaukakin sarki ya jikan wayanda suka rigamu gidan gaskiya."

Tijjani Ajiya ya ce:

"Subhanallah Allah ya kare gaba ya Jikan Wadanda suka rasu ya ba masu raunuka lafiya Ameen."

Muhammed So Sanadi Hdgg ya yi martani:

"Innanillahi waina ilaihim rajiun Allahumma ameen.

"Dama inaciki wanna masallacin yarifta mana.

"Allah y jikansu Da rahama."

Sani Shehu Daudawa ya ce:

"Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!
"Ubangiji Allah ya jiƙansu ya kyauta gaba."

Yunus Zakariyya Imam ya yi martani:

"Allahu Akbar. Allah ya jaddada rahamarsa agaresu."

Bazoum da dansa suna cikin mugun yanayi, ECOWAS

A wani labari na daban, kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika (ECOWAS) ta yi karin haske kan yanayin da hambararren shugaban kasar Nijar Mohamed Bazoum da dansa suke ciki.

Kwamishinan ECOWAS kan harkokin siysa, zaman lafiya da tsaro, Ambasada Abdel-Fatau Musah, ya ce Bazoum da dansa suna cikin mugun yanayi a tsare a hannun masu juyin mulki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng