Manyan Labarai A Yau
Wani lauya dan Najeriya, Abdulmalik, ya sha yabo a shafukan sada zumunta bayan ya gano masu wani gida da aka yi watsi da shi tsawon shekaru 30 a jihar Kaduna.
Gwamnatin shugaba Tinubu ta sanar da ware Naira biliyan 5 ga kowace jiha ciki har da babban birnin tarayya Abuja domin rage radadin cire tallafin man fetur.
Jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ta zargi gwamnatin jihar Kano da ba slƙalan kotun sauraron ƙararrakin zaɓen jihar cin hancin tsabar kuɗi har 10m.
Hedkwatar tsaro na kasa ta bayyana a ranar Alhamis, 17 ga watan Agusta cewa an kashe jami’an sojoji 36 a jihar Neja. Manjo Janar Edward Buba ne ya bayyana haka.
Fadar shugaban kasa ta sanar da ayyukan da aka bai wa zababbun ministoci, kuma ga mamakin mutane da dama Nyesom Wike aka bai wa ministan babban birnin tarayya.
Uwargidan shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, Remi Tinubu, ta janyo hankalin ƴan Najeriya da su tashi tsaye ba sai sun jira gwamnati ta yi musu komai ba a ƙasa.
Rikicin ƙabilanci ya ɓarke a tsakanin mayaƙan Boko Haram a jihar Borno. Mummunan rikicin ya sanya rayukan mayaƙan ƙungiyar ƴan ta'addan masu yawa sun salwanta.
Bayan rabawa gaba daya ministocin shugaban kasa Bola Tinubu ayyukan da za su yi, ya bayyana cewa shugaban Najeriyan ya yi watsi da shawarwarin Festus Keyamo.
Rahotanni sun tabbatar da ƴan bindiga sun kai wani mummunan hari kan wani sanannen fasto a birnin Benin, jihar Edo, inda suka raunata shi da halaka matarsa.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari