El-Rufai, Abba Gana: Cikakkun Sunayen Ministocin Babban Birnin Tarayya Tun 1999

El-Rufai, Abba Gana: Cikakkun Sunayen Ministocin Babban Birnin Tarayya Tun 1999

  • Babban birnin tarayya ita ce cibiyar hadin kai kuma gida da hedkwatar shugabanci a Najeriya
  • Tana dauke da fadar shugaban kasa da kujerar mulkin da ke jagorantar gaba daya gwamnonin jihohi 36, harda ministocin Abuja
  • A wannan zauren, Legit.ng ta jero tsoffin ministocin babban birnin tarayya tun daga 1999 da jihohinsu

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Abuja - A ranar Laraba, 16 ga watan Agusta, labari ya iso cewa an sanar da ayyukan gaba daya zababbun ministocin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu.

Jerin sunayen ya bai wa mutane da dama mamaki domin ayyukan da aka bai wa wasu ministocin ya sha banban da wanda masana harkokin siyasa da dama suka yi hasashe.

El-Rufai, Bala Mohammed suna daga cikin wadanda suka yi ministan Abuja
El-Rufai, Abba Gana: Cikakkun Sunayen Ministocin Babban Birnin Tarayya Tun 1999 Hoto: Nasir El-Rufai/Nyesom Ezenwo Wike/Senator Bala Abdulkadir Mohammed
Asali: Facebook

Daya daga cikin mukaman da suka ba da mamaki shine na tsohon gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike a matsayin ministan babban birnin tarayya Abuja.

Kara karanta wannan

Mukaman Ministoci: Yadda Shugaban Kasa Tinubu Ya Yi Watsi Da Keyamo, Ya Nada Kananan Ministoci 13

Wike shine dan kudu na farko da ya zama ministan Abuja tun bayan Mobolaji Ajose-Adeogun, ministan babban birnin tarayya na farko a 1976.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Jerin ministocin babban birnin tarayya

1. Ibrahim Bunu (1999 zuwa 2001) - jihar Borno

Ibrahim Bunu, dan jihar Borno, ya kasance shahararren mai zane wanda ya tsara dogayen gine-ginen NNPC a Abuja.

Yayin da Najeriya ta koma hannun mulkin dimokradiyya a shekarar 1999, Shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya nada Bunu mai shekaru 48 a matsayin minista na farko a babban birnin tarayya Abuja karkashin sabuwar mulkin dimokradiyya.

Kafin ya zama ministan babban birnin tarayya, Bunu ya taba rike mukamin karamin ministan gidaje da muhalli a shekarar 1982 a karkashin mulkin soja.

2. Mohammed Abba Gana (2001 zuwa 2003) - jihar Borno

Abba Ganna ya kasance sunan wani gida a FCT a zamanin da yake tashe. Kamar dai Bunu, shi ma dan jihar Borno ne, kuma injiniya ne.

Kara karanta wannan

Fadar Shugaban Kasa Ta Yi Karin Haske Kan Lokacin Da Tinubu Zai Rantsar Da Ministocinsa

Abba Gana wanda aka haifa a shekarar 1943, ya yi digirinsa a fannin injiniyan lantarki, a babbar jami’ar Ahmed Bello Zariya.

Shugaban kasa Olusegun Obasanjo ne ya nada shi ministan babban birnin tarayya Abuja a ranar 8 ga watan Fabrairun 2001. Daga baya ya zama mai ba mataimakin shugaban Najeriya Atiku Abubakar shawara na musamman kan kungiyoyin farar hula.

3. Nasir Ahmad El-Rufai (2003 zuwa 2007) - Jihar Kaduna

An haife shi a ranar 16 ga Fabrairu, 1960, ya fito ne daga jihar Kaduna, kuma ya taka rawar gani wajen gyarayanayin siyasar Najeriya.

El-Rufa'i wanda ke da ilimi a fannin tattalin arziki, ya rike mukamai daban-daban da suka hada da ministan babban birnin tarayya daga 2003 zuwa 2007, inda ya jagoranci zamanantar da babban birnin Najeriya, Abuja.

Shirin sabunta birane da ci gaban ababen more rayuwa shine abun da aka yi a mulkinsa, kuma ana daukarsa a matsayin ministan babban birnin tarayya da fi ba da mamaki a tarihi. Har yanzu ba a samu wanda ya yi aikinsa ba a Abuja.

Kara karanta wannan

“Bai Kamata Ya Zama Na Siyasa Kawai Ba”: Shehu Sani Ya Yi Martani Yayin da Tinubu Ya Nada Matawalle Ministan Tsaro

4. Aliyu Modibbo Umar (2007 zuwa 2008) - Jihar Gombe

Aliyu Modibbo Umar wanda aka haifa a ranar 15 ga watan Nuwamban 1958 ya fito daga Kumo a jihar Gombe. Ya mallami digiri a bangaren jarida daga jami'ar jihar Califonia Long Beach, digiri na biyu a ilimin Afrika, da kuma digiri na uku a bangaren ilimi daga jami'ar Califonia, Los Angeles (UCLA).

A lokacin da ya fara aiki da gwamnatin tarayya, Umar ya yi aiki da tashar NTA a shekarun 1970s. Daga nan ya koma Amurka a tsakiyar 80s, sannan ya dawo Najeriya, inda ya yi aiki a matsayin malamin jami'ar Abuja a 1993.

Bayan shekaru 10, shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya nada shi karamin ministan wuta da karafa. Daga baya ya yi aiki a matsayin ministan kasuwanci na dan gajeren lokaci kafin gwamnatin Shugaban kasa Umaru Musa Yar'adua ta sake nada shi a matsayin ministan Abuja.

Sai dai kuma zamansa ministan babban birnin tarayya bai yi wani tasiri ba saboda dan kankanin lokacin da ya yi a ofis.

Kara karanta wannan

Kyau Ya Hadu Da Kyau: Diyar Biloniya Indimi Ta Amarce Da Babban Dan Kasuwar Kasar Turkiyya

5. Muhammadu Adamu Aliero (2008 zuwa 2010) - Jihar Kebbi

Muhammadu Adamu Aliero, ya kasance gwamnan jihar Kebbi sau biyu daga 1999 zuwa 2007 kafin aka nada shi minista.

Ya shahara sosai wajen sauya sheka daga wannan jam’iyya zuwa waccan domin biyan bukatarsa ​​da kuma ra'ayinsa na siyasa.

A ranar 17 ga watan Disambar 2008, Shugaba Goodluck Jonathan ya nada shi ministan babban birnin tarayya Abuja. Wa'adinsa na minista bai wuce shekara biyu ba inda ya zama mutum na biyu da ya yi gwagwarmayar kaiwa matsayin tsohon minista Nasir El-Rufai.

6. Bala Mohammed (2010 zuwa 2015) - Jihar Bauchi

Bala Mohammed dan siyasa ne haifaffen Bauchi wanda ake matukar mutunta kwarewarsa a aikin gwamnati a fadin kasar.

An haifi Mohammed a ranar 5 ga Oktoban 1958, Mohammed ya fara aikinsa tare da gwamnati da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN). Ya shiga aikin gwamnati ne a shekarar 1984 lokacin da aka dauke shi aiki a matsayin jami’in gudanarwa a karkashin ma’aikatar harkokin cikin gida ta tarayya, a Abuja.

Kara karanta wannan

Daga karshe: Malaman Izala sun dira Nijar don neman hanyar sulhu a batun juyin mulki

A wancan lokutan, an kara masa girma zuwa ma’aikacin gwamnati a ma’aikatu da dama. Sai dai ya zama cikakken dan siyasa a matsayin Sanata mai wakiltar Bauchi ta Kudu daga 2007 zuwa 2010.

Shugaban kasa Goodluck Jonathan ne ya nada shi ministan babban birnin tarayya Abuja a ranar 8 ga Afrilun 2010 kuma ya ci gaba da rike mukamin har zuwa ranar 29 ga watan Mayun 2015. Wa’adinsa na minista ya cimma nasara, amma bai kai ga samun nasarar Nasir El-Rufai ba.

7. Mohammed Musa Bello (2015 zuwa 2023) - Jihar Adamawa

Mohammed Musa Bello ya fito daga jihar Adamawa ne kuma an haife shi a gidan Fulani na Alhaji Musa Bello, tsohon Manajan Daraktan Kamfanin Raya Arewacin Najeriya daga 1970 zuwa 1976.

Bello shi ne ministan babban birnin tarayya Abuja mafi dadewa a tarihi, inda ya kwashe shekaru takwas yana mulki daga 2015 zuwa 2023.

A unguwannin Abuja, ana masa kallon minista mafi muni a babban birnin tarayya Abuja. Ba shi da farin jini, kuma har daliban firamare ba su san shi ba. Tsafta da kwanciyar hankalin Abuja ya canza a lokacin mulkinsa, babban birni ya cika da datti. Zamaninsa ya tara ayyuka da dama da aka yi watsi da su da wadanda ba a kammala ba.

Kara karanta wannan

Obasanjo Ya Bayyana Malamin Addinin Kirista a Najeriya Ɗaya Tak Da Zai Shiga Aljanna

Mukaman Ministoci: Yadda Shugaban Kasa Tinubu Ya Yi Watsi Da Keyamo, Ya Nada Kananan Ministoci 13

A wani labarin, mun ji cewa bayan rabawa ministocin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu mukamai da aka yi a ranar Laraba, 17 ga watan Agusta, ya nuna cewa shugaban Najeriyan ya yi watsi da tangardar da Festus Keyamo ya gano.

Keyamo, babban lauyan Najeriya (SAN), ya kasance karamin ministan kwadago da daukar ma'aikata a lokacin gwamnatin Muhammadu Buhari.

Asali: Legit.ng

Online view pixel