Jam'iyyar APC Ta Zargi Gwamnatin Kano Da Bayar Da Cin Hancin N10m

Jam'iyyar APC Ta Zargi Gwamnatin Kano Da Bayar Da Cin Hancin N10m

  • Jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ta bankaɗo wani shiri da gwamnatin jihar Kano ta ke yi kan shari'ar zaɓen gwamnan jihar
  • Jam'iyyar APC ta zargi gwamnatin Abba Gida-Gida da yunƙurin ba alƙalan da ke sauraron shari'ar cin hancin N10m
  • APC ta ce gwamnatin jihar ta hango rashin nasara ƙarara a kotun shiyasa ta fara wasu ƴan ƙananan maganganu kan shari'ar zaɓen

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Kano - Jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ta ja kunnen gwamnatin jihar Kano da ta guji kunyata shugabar kotun sauraron ƙararrakin zaɓukan ƴan majalisun jiha da na tarayya a jihar, mai shari'a Flora Aringe.

Gargaɗin na zuwa ne biyo bayan zargin tayin cin hancin N10m da aka yi wa wasu daga cikin alƙalan kotun, cewar rahoton The Punch.

APC ta zargi gwamnatin Kano ta bada cin hancin N10m
Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakin yaƙin neman zaɓen Gawuna-Garo, Malam Muhammad Garba, ya fitar.

Kara karanta wannan

Ganduje Ya Bayyana Abin Da APC Za Ta Yi Wa Jam’iyyun Adawa a Karkashin Jagorancinsa

Hakan na zuwa ne bayan gwamnatin jihar Kano ta yi kira ga jami'an tsaro da su gudanar da bincike mai zurfi kan zargin da tare da gurfanar da masu hannu a ciki waɗanda sun yi ƙaurin suna wajen bada cin hanci.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

APC ta zargi gwamnatin Kano

Da yake mayar da martani, Garba, wanda shi ne tsohon kwamishinan watsa labarai na jihar, ya bayyana cewa kalaman na gwamnatin Kano wani ƙoƙari ne kawai na cin mutuncin jam'iyyar APC da kotun.

Ya kuma yi zargin cewa ƙoƙarin da gwamnatin ta yi na kunyata shugabar kotun, ya faru ne bisa tsoron da take na yiwuwar shan kashi a shari'ar da ake yi a kotun.

A kalamansa:

"Gwamnatin jihar Kano ta fara jin tsoron kotu za ta bayyana ainihin wanda ya bayar da cin hancin, shiyasa ta fara ƙoƙarin yi wa mai shari'ar ƙarya."

Kara karanta wannan

Cin Hanci: Abba Gida Gida Ya Tsorata, Ya Bukaci Binciken Gaggawa A Kotun Sauraran Korafe-Korafen Zabe

"Labarin da suka ƙirƙiro wanda yana cikin wata sanarwa da kwamishinan watsa labarai, Baba Halili Dantiye ya fitar, ya ƙara tabbatar da cewa gwamnatin na ƙoƙarin ɓata sunan kotun ne kafin yanke hukunci domin jama'a su tausaya mata idan ta yi rashin nasara."

Garba ya cigaba da cewa, jam'iyyar APC ba za ta taɓa bayar da cin hanci ba kan shari'ar saboda alamun nasara yana tattare da ita.

Barau Ya Nemi Addu'ar 'Yan Najeriya

A wani labarin kuma, mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barai Jibrin ya nemi ƴan Najeriya su taya jam'iyyar APC addu'a.

Barau ya buƙaci addua'ar ne domin samun nasara a shari'ar zaben gwamnan Kano da jam'iyyar ke yi da gwamnatin jihar ta jam'iyyar NNPP.

Asali: Legit.ng

Online view pixel