Gwamnan Jihar Neja Na Duba Yiwuwar Tattaunawa Da 'Yan Bindiga

Gwamnan Jihar Neja Na Duba Yiwuwar Tattaunawa Da 'Yan Bindiga

  • Gwamnan jihar Neja ya koka kan yadda hare-haren ƴan bindiga su ke ƙara yawaita a jihar ba ƙaƙƙautawa
  • Gwamna Mohammed Bago ya bayyana cewa gwamnatinsa na duba yiwuwar hawa kan teburin sulhu da ƴan bindiga
  • Sa dai, gwamnan ya bayar da tabbacin cewa idan tattaunawar ba ta yiwu ba, za a yi amfani da ƙarfin soja akan ƴan bindigan

Jihar Neja - Gwamnan jihar Neja, Mohammed Umaru Bago, ya bayyana cewa gwamnatinsa na duba yiwuwar yin sulhu da ƴan bindiga a jihar.

Gwamnan ya bayyana hakan ne bayan ya sanya labule da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, cewar rahoton The Guardian.

Gwamnan Neja na duba yiwuwar tattauna da 'yan bindiga
Gwamnan jihar Neja, Mohammed Umaru Bago Hoto: @HonBago
Asali: Twitter

Bago wanda ya tattauna da manema labarai bayan kammala ganawarsa da Tinubu, ya koka kan yadda lamarin tsaro a jihar Neja ya taɓarɓare.

Kara karanta wannan

Tinubu Ya Ba 'Yan Najeriya Haƙuri, Ya Fadi Sabbin Matakan Rage Raɗaɗin Da Ya Dauka

Dalilin son yin sulhu na gwamna Bago

A kalamansa:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Ba mu son wani aikin soja sosai a jihar Neja kamar yadda ba mu son makiyaya su bar jihar mu saboda kasuwanci da zuba hannun hari.".
"Amma idan ba mu kai matakin tattaunawa ba, lallai dole mu yi amfani da dukkanin ƙarfin soja."

A cikin ƴan kwanakin nan dai jihar Neja ta fuskanci hare-haren ƴan bindiga da ƴan ta'adda, waɗanda suka halaka mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba.

Manoma sun sha wuya a hannun ƴan bindiga

Bago ya bayyana cewa manoma su ne waɗanda rikicin ya fi shafa, inda da yawa daga cikinsu sun bar gonakinsu saboda tsoron kai musu farmaki.

Gwamnan ya yi magana kan illar da ƴan bindiga, barayin shanu, masu haƙar ma'adanai ba bisa ƙa'ida da sauran miyagu suka haifar kan al'ummar jihar.

Kara karanta wannan

Yan Bindiga Sun Kai Hari a Wata Jiha Sun Yi Awon Gaba Da Wasu Ma'aurata

"Ana yi wa jihar Neja kallon inda ya fi ko ina yin noma a Najeriya saboda yawan faɗin ƙasar noma da mu ke da ita, wacce gwamnati da sauran al'umma da dama ke amfana da ita." A cewarsa.
"Amma taɓarɓarewar tsaro ya sanya mutanen mu yanzu suna fargabar ƴan bindiga da sauran miyagu masu aikata laifuka."

A cikin ƴan kwanakin nan ne dai ƴan bindiga suka yi wa sojoji kwanton ɓauna a yankin Shiroro na jihar, yayin da a ranar Litinin wani jirgin sojojin saman Najeriya ya yi hatsari.

'Yan Gudun Hijira a Neja Sun Kai 5,000

A wani labarin kuma, mataimakin gwamnan jihar Neja ya bayyana adadin yawan mutanen da suka zama ƴan gudun hijira a jihar.

Yakubu Garba ya bayyana hakan ne lokacin da ya kai ziyara ofishin hukumar bayar da agajin gaggawa ta ƙasa (NEMA) a birnin tarayya Abuja.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel