Gwamna Bago Ya Ce Gidan Yari Zai Tura Wadanda Suka Karkatar Da Kayan Tallafi

Gwamna Bago Ya Ce Gidan Yari Zai Tura Wadanda Suka Karkatar Da Kayan Tallafi

  • Gwamnan jihar Neja ya shirya ɗaukar mummunan mataki kan duk waɗanda suka kuskura suka karkatar da kayan tallafi
  • Gwamna Mohammed Umaru Bago ya bayyana cewa duk wanda ya kuskura ya karkatar da kayan sai ya tafi gidan yari
  • Gwamnan ya kuma bayar da hutun kwanaki uku domin ma'aikata su samu damar sanya ido kan rabon kayan tallafin

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Neja - Gwamnan jihar Neja, Mohammed Umaru Bago, ya bayyana hukuncin da zai ɗauka kan waɗanda suka kuskura suka karkatar da kayan tallafin da gwamnatin tarayya ta bayar a raba a jihar.

Gwamna Bago ya bayyana cewa sai ya sanya an ɗaure duk wanda ya kuskura ya karkatar da kayan tallafin a gidan gyaran hali, komai girman matsayin da ya ke da shi, rahoton Aminiya ya tabbatar.

Gwamna Bago zai hukunta wadanda suka karkatar da kayan tallafi
Gwamna Bago zai tura wadanda suka karkatar da kayan tallafi zuwa gidan yari Hoto: @GovBago
Asali: Twitter

Gwamnan a yayin ganawa da ƴan jarida ya bayyana cewa daga jami'an gwamnati zuwa sarakunan gargajiya, babu wanda zai tsira daga tafiya gidan yari idan har aka same shi da laifin karkatar da kayan tallafin.

Kara karanta wannan

Gwamnan Arewa Dauki Yan Sa Kai 7,000 Aiki Don Magance Matsalar Rashin Tsaro

Gwamna Bago ya kuma bayar da hutun kwana uku domin ma'aikatan jihar su samu damar zuwa karɓar kayan tallafin waɗanda suka kai na kimanin kuɗi naira biliyan 3.6.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnan ya bayyana cewa hutun na ranakun Laraba, Alhamis da Juma'a, zai sanya ma'aikata da masu riƙe da muƙaman siyasa damar komawa mazaɓunsu, domin su sanya ido wajen ganin an yi gaskiya da adalci wajen rabon kayan tallafin.

Gwamna Bago ya bukaci taimakon sarakuna

Gwamnan ya kuma buƙaci sarakunan gargajiya, malaman addini da ƴan jarida da su sanya ido kan yadda za a yi rabon kayan a yankunansu domin tabbatar da cewa waɗanda yakamata su samu tallafin sun samu.

Gwamna Bago ya kuma bayyana cewa gwamnatin tarayya ta ba jiharsa kuɗi naira biliyan biyu da motoci biyar na hatsi, amma suna jiran ƙarin buhunan masara 40,000 da kuɗi naira biliyan biyu.

Kara karanta wannan

Gwamna Uba Sani Ya Dau Zafi Kan Kisan Masallata a Kaduna, Ya Ba Jami'an Tsaro Muhimmin Umarni

Legit Hausa ta samu jin ta bakin wata ƴar jihar Neja mai suna Joy Sokolayam wacce ta yaba da wannan matakin da gwamnan ya ke shirin ɗauka.

Joy ta bayyana cewa wannan matakin na gwamnan zai taimaka wajen sanya tsoro a zukatan masu niyyar karkatar da kayan tallafin.

"Wannan shi ne abin da yakamata a yi domin kayan nan an kawo su ne domin a raba ga al'umma, bai kamata wasu su yi handama da baba-kere kan kayayyakin ba." A cewarta.

Gwamna Bago Ya Ba Mata Mukamai

A wani labarin kuma gwamnan jihar Neja, Mohammed Umaru Bago, ya gwangwaje mata da muƙamai a jihar.

Gwamna ya naɗa hadimai mata guda 131 a jihar domin damawa da su a cikin harkokin tafiyar da mulkin jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel