‘Abun da Tinubu ya Fada Mani Bayan Nada Ni Ministan Abuja’, Wike Ya Bayyana

‘Abun da Tinubu ya Fada Mani Bayan Nada Ni Ministan Abuja’, Wike Ya Bayyana

  • Nyesom Wike, ministan babban birnin tarayya Abuja ya ce Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu bai bayyana takamaiman abun da yake tsammani daga gare shi ba
  • Sai dai Wike ya ce shugaban kasar na muradin farfado da Abuja kuma hukumar babbar birnin tarayya na aiki tukuru don cimma wannan manufar
  • Ministan ya bayyana cewa Shugaban kasa Tinubu yana da sha’awar a kammala aikin layin dogo na Abuja cikin watanni takwas

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT, Abuja - Nyesom Wike, ministan babban birnin tarayya Abuja, ya ce Shugaban kasa Bola Tinubu ya umurce shi da ya "dawo da birnin".

Da yake jawabi a wata hira da Channels TV a ranar Laraba, 30 ga watan Agusta, tsohon gwamnan na jihar Ribas ya ce ya samu umurni daga shugaban kasa Tinubu cewa ya farfado da babban birnin tarayya.

Kara karanta wannan

Dalilin Da Yasa Na Yi Mamaki Da Tinubu Ya Nada Ni Ministan Abuja, Wike

Tinubu ya bukaci Wike ya farfado da Abuja
‘Abun da Tinubu ya Fada Mani Bayan Nada Ni Ministan Abuja’, Wike Ya Bayyana Hoto: Willy Ibimina Jim-george
Asali: Facebook

Wike ya magantu kan umurnin Buhari

A cewar ministan, daya daga cikin muhimman abubuwan da ake bukata a babban birnin tarayyar Najeriya shi ne titin jirgin kasa na Abuja.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ya ce:

"Abun da ya fada mani, ya ajiye shi, 'Ina so ka dawo da birnin'.
"Bai fadi wannan ba, kada ya zamana kamar 'ai yana da wani abu a zuciya'.
“Abu guda da ya fito fili ya fada, Ina kallon shi inda ya fadi a taron kungiyar lauyoyi na NBA, ‘Ya uban gidan Abuja, ina so na shiga jirgin kasa a tuka ni’.
"Na tuna, kafin nadi na, lokacin da na samu damar tattaunawa da shi, ba tare da na san cewa zai tura ni babban birnin tarayya bane, ya ce 'duba wannan da wannan, akwai layin dogo'. Bai zo mani cewa karin haske bane. Na zata muna dai tattaunawa ne gaba daya"

Kara karanta wannan

Ministan Abuja: Tsohon Gwamnan PDP Ya Fayyace Gaskiyar Wanda Yake Wa Aiki Tsakanin Tinubu da APC

"Uban gidan Abuja, ina so na shiga jirgin kasan ka a tuka ni' abun da shugaban kasar ya fadi kenan a taron kungiyar lauyoyi na NBA, shin wannan ba umurni bane?"

Na yi mamakin nada ni ministan Abuja, Wike

A wani labarin kuma, ministan Abuja, Nyesom Wike, ya ce bai taba tsammanin za a nada shi a matsayin ministan babban birnin tarayya ba.

Wike ya ce sam bai sa rai a wannan kujera ba ko daidai da rana daya ba don haka da ya ji labarin shi aka ba ministan FCT sai ya cika da mamaki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel