Manyan Labarai A Yau
Wata mahaifiya ta yi ta maza inda ta cafke wani ɗan ta'adda da ya save ɗiyarta sannan ya halaka ta bayan an ba shi kuɗin fansa masu yawa a Zariya.
Kungiyar SERAP ta maka gwamnonin Najeriya 36 ƙara a gaban kotu inda ta nemi a tilasta su bayar da bayanai kan yadda suka kashe kuɗaɗen tallafin da suka amsa daga FG.
Gwamnan jihar Sokoto, Ahmed Aliyu ya yi magana kan nasarar da ya samu a kotun zaɓen gwamnan jihar. Gwamnan ya yaba da hukuncin kotu inda ya shawarci ƴan adawa.
Ɗan takarar ɗan majalisar dokokin jihar Delta a ƙarƙashin inuwar jam'iyyar Labour Party (LP), ya koka kan yadda ya kasa biyan basussukan da ya ci a lokacin zaɓe.
Rundunar ƴan sandan jihar Katsina ta tabbatar da cafke wasu ɗalibai ma jami'ar gwamnatin tarayya da ke Dutsinma, bisa zargin hannu a mutuwar abokin karatunsu.
An shawarci jam’iyyar NNPP da gwamnatin jihar Kano da aka tsige da su shirya ma wani zaben a nan da shekaru hudu masu zuwa maimakon barazana ga bangaren shari’a.
An samu asarar ran mutum ɗaya bayan rufin wani gini ya rufto kan wani gini da ba a kammala aikinsa ba a jami'ar jihar Taraba da ke birnin Jalingo.
Kotun sauraron ƙararrakin zaɓen gwamnan jihar Sokoto ta tabbatar da nasarar da gwamna Ahmed Aliyu na jam'iyyar APC ya samu a zaɓen gwamnan jihar.
An hana wasu kafafen yada labarai masu zaman kansu shiga harabar kotu domin yanke hukuncin karshe na kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan jihar Sokoto.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari