Manyan Labarai A Yau
Wasu mutane da ba a san ko wanene ba, sun halaka diyar dan majalisar dokokin jihar Borno a gidan mijinta. Lamarin mara daɗin ji ya auku ne a birnin Maiduguri.
Ƙungiyoyin ƙwadago na NLC da TUC sun ba gwamnoni 36 na ƙasar nan wa'adin makonni biyu kan aiwatar da ƙarin albashin N35,000 ga ma'aikata a jihohinsu.
Gwamnatin jihar Ondo ta yi magana kan rahotannin da ke yawo kan cewa ana shirye-shiryen sake fitar da gwamna Rotimi Akeredolu zuwa ƙasar waje neman lafiya.
Majalisar dattawan Najeriya za ta tantance sabon shugaban hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arziƙin ƙasa zagon ƙasa (EFCC), Olanipekun Olukoyede, a ranar Laraba.
Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya rushe shugabannin gudanarwa na hujumar Alhazai ta ƙasa (NAHCON). Shugaban ƙasar ya kuma naɗa sabon shugaban hukumar.
Dakta Musa Adamu Aliyu ya zama sabon shugaban hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta ICPC. Hakan na zuwa ne bayan naɗin da Shugaba Tinubu ya yi masa.
An karrama dan Najeriya mai shekaru 70 da ya kirkiri janareto mara amfani da mai da digirgir. Mallam Hadi Usman ya kuma kirkiri risho mai girki da ruwa.
Tsohon sakataren jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a jihar Ƙwara, Alhaji Rasaq ya tattara ƴan komatsansa zuwa jam'iyyar APC mai mulki a jihar.
An rahoto cewa Shugaban kasa Bola Tinubu ya nada Fatima Faruk a matsayin babbar mai ba shi shawara kan harkokin mata. An sanar da hakan ne a ranar Litinin.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari