Kungiyoyin Kwadago Sun Ba Gwamnonin Jihohi 36 Wa'adin Makonni Biyu Kan Karin Albashin N35,000

Kungiyoyin Kwadago Sun Ba Gwamnonin Jihohi 36 Wa'adin Makonni Biyu Kan Karin Albashin N35,000

  • Ƙungiyar ƙwadago ta bayar da wa'adin mako biyu ga gwamnoni su fara tattaunawa kan batun biyan albashin N35,000 a jihohinsu
  • A cewar ƙungiyar, yarjejeniyar da aka cimma tsakanin gwamnatin tarayya da shugabannin NLC da TUC a ranar 1 ga watan Oktoba ta shafi jihohin
  • Ƙungiyar kwadagon dai ta yi barazanar shiga yajin aikin gama-gari a ranar 3 ga watan Oktoba kan batun cire tallafin man fetur, amma bayan yarjejeniyar ta janye batun

FCT, Abuja - Ƙungiyar ƙwadago ta ba gwamnoni 36 na ƙasar nan wa'adin mako biyu kan su fara tattaunawa da mambobinta kan biyan ƙarin albashin N35,000 ga ma'aikata a jihohinsu.

Kamar yadda jaridar The Punch ta ruwaito, ƙungiyoyin ƙwadagon na neman jihohin da su tattauna da ma'aikatansu bisa yarjejeniyar fahimtar juna da aka cimma tsakanin ƙungiyoyin ƙwadago na NLC da TUC da gwamnatin tarayya.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Jihar APC Ta Yi Magana Kan Batun Sake Fitar da Gwamna Mara Lafiya Kasar Waje Domin Jinya

Kungiyoyin kwadago sun ba gwamnoni wa'adin makonni biyu
Kungiyoyin kwadago sun ba gwamnoni wa'adin makonni biyu kan karin albashi Hoto: Abdulrahman Abdulrasaq, NLC
Asali: Twitter

Ƙungiyoyin NLC da TUC sun miƙa wa gwamnonin wa'adin ne a ranar Talata, 17 ga watan Oktoba, inda suka bukaci gwamnonin da su gaggauta bin ƙa'idojin da suka dace wajen aiwatar da shirin domin rage raɗaɗin cire tallafin man fetur.

Wacce buƙata ƙungiyoyin ƙwadagon suka nema?

Ƙungiyoyin ƙwadagon sun ce wa'adin biyan albashin ma'aikatan zai ƙare nan da makonni biyu, domin haka akwai buƙatar gwamnoni su fara aiwatar da shi cikin gaggawa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ƙungiyoyin NLC da TUC a matakin tarayya sun cimma yarjejeniya da gwamnatin tarayya a ranar 1 ga watan Oktoba domin ma'aikata su samu ƙarin albashin N35,000 har sai an sanya hannu kan sabon mafi ƙarancin albashi na ƙasa.

Haka kuma, ƙungiyar da gwamnati sun amince cewa za a biya ma'aikatan tarayya ƙarin albashin har na tsawon watanni shida yayin da aka buƙaci gwamnonin da su ɗauki irin wannan matakin da zai amfani ma'aikata.

Kara karanta wannan

Shiri Ya Yi Kyau: Jiragen Yakin Sojin Sama Sun Halaka Yan Ta'adda da Dama a Wani Luguden Wuta da Suka Yi Musu

Tun da farko dai ƙungiyar ƙwadagon ta yi barazanar fara yajin aiki a faɗin ƙasar nan a ranar 3 ga watan Oktoba, amma gwamnati ta samu damar dakatar da wannan yunƙurin bayan sun cimma yarjejeniya.

NLC Ta Magantu Kan Mafi Karancin Albashi

A wani labarin kuma, ƙungiyar ƙwadago ta yi magana kan mafi ƙarancin albashin da za ta tattauna nan gaba da gwamnatin tarayya.

Ƙungiyar ta bayyana cewa mafi ƙarancin albashin da gwamnatin tarayya za ta riƙa biya shi ne naira dubu 100 zuwa 200 saboda yadda rayuwa ta ƙara tsada.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel