Yan Bindiga Sun Halaka Mutum 3 da Sace Hakimi a Jihar Zamfara

Yan Bindiga Sun Halaka Mutum 3 da Sace Hakimi a Jihar Zamfara

  • Ƴan bindiga sun kai wanu mummunan farmaki a ƙauyen Bagega da ke ƙaramar hukumar Anka ta jihar Zamfara
  • Migayun ƴan bindiga sun halaka mutum uku tare da raunata wasu mutane da dama a yayin harin da suka kai
  • Haka kuma sun yi garkuwa da Hakimin ƙauyen, ƴarsa da wasu tarin mutane masu yawa a mummunan harin

Jihar Zamfara - Aƙalla mutum uku ne suka mutu sannan wasu 11 suka jikkata a wani hari da wasu ƴan bindiga suka kai a ƙauyen Bagega da ke ƙaramar hukumar Anka a jihar Zamfara.

A yayin harin, ƴan bindigan sun yi awon gaba da hakimin ƙauyen, da ƴarsa mai shekara takwas da kuma wasu kimanin mutum 10, cewar rahoton TRT Afrika.

Yan bindiga sun kai sabon hari a Zamfara
Yan bindiga sun halaka mutum uku da sace hakimi a Zamfara Hoto: Theguardian.com
Asali: UGC

Wani mazaunin ƙauyen da ya tsere a lokacin harin mai suna Abdullahi Bagega, ya shaida wa Channels tv a ranar Laraba cewa, ƴan bindigan sun mamaye ƙauyen ne a kan babura a yammacin ranar Litinin, 16 ga watan Oktoba.

Kara karanta wannan

Yan Bindiga Sun Yi Wa Jami'an Tsaro Kwanton Bauna a Jihar Arewa, Sun Halaka Da Dama Daga Cikinsu

Yadda ƴan bindigan suka kawo harin

Abdullahi ya yi nuni da cewa ƴan bindigan na isowa suka fara harbe-harben bindiga, wanda hakan ya tilasta wa mazauna ƙauyen guduwa domin tsira da rayukansu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce an kashe mutum uku, wasu mutum 11 kuma sun samu munanan raunuka, inda ake ba su kulawa a asibitoci daban-daban.

Abdullahi ya ƙara da cewa har yanzu ba a ga wasu mazauna ƙauyen ba da suka gudu a lokacin harin.

A kalamansa:

"Sun yi garkuwa da Sarkin Gabas na ƙauyenmu da ƙaramar ƴarsa ƴar kimanin shekara takwas, wasu mutum shida da mutum huɗu daga wani ƙauye a kusa da Bagega. Adadin bai kai mutum 50 ba. Yanzu haka muna da mutum 11 da suka samu munanan raunuka."

Kakakin rundunar ƴan sandan jihar bai tabbatar da aukuwar harin ba lokacin da aka tuntuɓesa, amma ya yi alƙawarin bayar da bayanai idan ya yi bincike domin sanin abin da ya auku.

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Shiga Ƙaramar Hukuma 1 a Jihar Kano, Sun Kashe Mutane Sun Sace Wasu da Yawa

An Halaka Diyar Dan Majalisa

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu miyagun sun aikaka kisan gilla kan ɗiyar wani ɗan majalisar dokokin jihar Borno a gidan mijinta.

Miyagun dai sun halaka marigayiyar ne bayan sun ɗaure mata hannayenta ta baya da ƙafafunta, sannan suka shaƙe ta har sai da ta daina numfashi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel