Mataimakin Kwamishinan Yan Sandan Jihar Bayelsa Ya Rasu

Mataimakin Kwamishinan Yan Sandan Jihar Bayelsa Ya Rasu

  • Runɗunar ƴan sandan jihar Bayelsa ta yi babban rashin ɗaya daga cikin manyan jami'anta wanda ya mutu yana tsaka da barcinsa
  • Mataimakin kwamishinan ƴan sandan jihar, ACP Oluseye Odunmbaku, ya yi bakwana da duniya a ranar Asabar, 14 ga watan Oktoban 2023
  • Marigayin wanda ba a bayar da cikakkun bayanai kan mutiwarsa ba, an bayyana shi a matsayin jajirtaccen jami'i mai kishi wajen gudanar da aikinsa

Jihar Bayelsa - Wani mataimakin kwamishinan ƴan sanda a Bayelsa, ACP Oluseye Odunmbaku, ya riga mu gidan gaskiya.

Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa ACP Odunmbaku ya mutu ne bayan ya kwanta barci a gidansa da ke Yenagoa, babban birnin jihar Bayelsa.

Mataimakin kwamishinan yan sanda ya rasu
Mukaddashin Sufeto Janar na yan sanda, Kayode Adegbotekun Hoto: Nigeria Police Force
Asali: Facebook

Kakakin rundunar ƴan sandan jihar Bayelsa, CSP Asinim Butswat, wanda ya tabbatar da rasuwar babban jami'in ƴan sandan, bai bayar da cikakken bayani ba.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Gwamna Zulum Ya Bayar da Muhimmin Umarni Bayan Miyagu Sun Halaka Diyar Dan Majalisa a Jihar Borno

Hukumomi sun tabbatar da rasuwarsa

Butswat a cikin wata ƴar gajeruwar sanarwa ya bayyana cewa:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Rundunar ƴan sandan jihar Bayelsa na baƙin cikin sanar da rasuwar ACP Oluseye Odunmbaku, har ya zuwa lokacin rasuwarsa shi ne mataimakin kwamishinan ƴan sanda, sashen ayyuka."

Ko da yake babu cikakkun bayanai game da mutuwarsa, abokan aikinsa sun aike da ta'aziyyar mutuwarsa.

Ɗaya daga cikinsu ya bayyana shi a matsayin jami'i mai himma wanda ya bayar da iyakacin ƙoƙarinsa ga rundunar ƴan sanda wajen tabbatar da tsaro da kare dukiyoyi.

Jaridar Punch ta fahimci cewa marigayin ya mutu ne a ranar Asabar, 14 ga watan Oktoban 2023.

Malamin jami'a ya rasu yana cikin barci

Wani malami a Jami'ar Jihar Kwara, da ke Melete, Dakta Ajeibe Issa, ya mutu lokacin da yake barci a gidansa da ke Ilorin, babban birnin Jihar Kwara, da safiyar Litinin.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Jihar APC Ta Yi Magana Kan Batun Sake Fitar da Gwamna Mara Lafiya Kasar Waje Domin Jinya

Har zuwa rasuwarsa, Yakub shi ne shugaban sashen koyar da lafiyar dan adam da ilimin kiwon lafiya na cibiyar sannan kuma ya kasance daraktan wasanni na riko.

Babban Alkalin Kwara Ya Riga Mu Gidan Gaskiya

A wani labarin kuma, Alƙalin babbar kotun jihar Kwara, mai shari'a Sikiru Adeyinka Oyinloye ya riga mu gidan gaskiya.

Marigayin ya yi bankwana da duniya yana da shekara 58 bayan ya daɗe yana fama da ciwo wanda ya shafi wuyansa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel