Manyan Labarai A Yau
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi wa tagwayen da aka haifa a hade fatan nasara a tiyatar da za a yi masu yayin da suka bar Kano zuwa kasar Saudiyya don ayi masu aiki.
Wasu miyagun ƴan bindiga ɗauke da makamai sun kai farmaki a wasu ƙauyukan jihar Benue guda biyu. Ƴan bindigan a yayin harin sun halaka mutum bakwai.
Mayaƙan ƙungiyar ƴan ta'addan Boko Haram sun kai mummunan farmaki a jihar Borno. Ƴan ta'addan sun halaka babban limamin ƙaramar hukumar Kaga da wani ɗan sakai.
Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Atiku Abubakar, ya yi magana a karon farko bayan rashin nasarar da ya yi a kotun ƙoli.
Gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara, ya yi zargin cewa an haɗa baki da jami'an tsaron jihar. Hakan na zuwa ne yayin da ake cigaba da shirin tsige shi.
Bayanai sun nuna cewa gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara, ya samu takardar shirin tsige shi daga majalisar dokokin jihar, a cigaba da rikicin siyasar jihar.
Magoya bayan gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara, sun yi dafifi zuwa majalisar dokokin jihar yayin da aka fara shirye-shiryen tsige shi daga muƙamin gwamna.
Wasu miyagun ƴan bindiga ɗauke da makamai sun kai farmaki a jihar Taraba inda suka yi awon gaba da wani babban faston Katolika da wasu mutum biyu.
Ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa (NLC) ta yi barazanar ƙin halartar taron da za su yi da gwamnatin tarayya idan ministan ƙwadago, Simon Lalong, zai halarci zaman.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari