Manyan Labarai A Yau
Rundunar yan sandan jihar Katsina ta tabbatar da halaka yan bindiga 13 da ceto mutane masu yawa da aka yi garkuwa da su a jihar. Sun kwato kayayyaki masu yawa.
Shugaban kasa Bola Tinubu ya tsige akalla manyan jami’an gwamnati tara a cikin sa’o’i 24. Yawancinsu gwamnatin Shugaban kasa Muhammadu Buhari ce ta nada su.
Tony Adoki daya daga cikin yan majalisar dokokin jihar Rivers ya yi magana kan sake komawa PDP, yan kwanaki kadan bayan ya sauya sheka zuwa jam'iyyar APC.
Kungiyar MURIC ta yi magana kan masu sukar tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari. Kungiyar ta yi nuni da cewa Buhari ya yi ayyuka sosai a kasar nan.
Zacchaeus Adangor, Atoni janar kuma kwamishinan shari'a na jihar Ribas, ya yi murabus daga mukaminsa ana zaune kalau. Ya rubuta wasika ga Gwamna Sim Fubara.
Mai shari’a Abdulaziz Waziri na kotun daukaka kara ya bayyana ainahin dalilin da yasa aka tsige yan majalisar jihar Filato 16, yana mai karin haske kan hukuncin.
Jam’iyyar PDP a jihar Oyo tana shirin kara samun gagarumin karfi yayin da Shina Peller, tsohon dan majalisar wakilai kuma tsohon jigon APC ke shirin komawa cikinta.
Gwamnan jihar Katsina, Mallam Dikko Umar Radda, a ranar Laraba ya raba N450m ga makarantun sakandare 100 a fadin jihar domin bunkasa harkokin ilmi.
Wani malamin addini mazaunin Abuja, Fasto Joshua Iginla ya yi hasashen abun da zai faru a shekarar 2024. Malamin addinin ya ce abun zai ba mutane mamaki.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari