Manyan Labarai A Yau
Mukaddashin gwamnan jihar Ondo, Lucky Aiyedatiwa, ya bayar da umarnin kulle asusun kananan hukumomin jihar jim kadan bayan ya hau kujerar mulkin jihar.
Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasir Ahmed El-Rufai, ya na ɗab da kafa tarihi inda zai zama dan Arewa na farko da ya samu mukamin sarauta a Ijebu.
Kungiyar matasa marasa aikin yi a Najeriya (CUYN) ta yaba da ayyukan da ministar ayyukan jin kai da kawar da fatara, Dr Beta Edu, bayan ta hau kan kujera.
Babban Hafsan Hafsoshin Sojojin Najeriya (CDS), Janar Christopher Gwabin Musa, ya sha alwashin gano bakin zaren harin bam da sojojin Najeriya suka kai.
Sashen kula da lafiyar jama’a na Chicago ya ambaci sunan yar Najeriya Dr. Olusimbo Ige a matsayin kwamishina inda ta zama bakar fata mace ta farko kan wannan mukami.
Rikicin siyasa jihar Rivers na cigaba da daukar zafi tsakanin Gwamna Siminalayi Fubara da magabacinsa Nyesom Ezenwo Wike, ministan birnin tarayya Abuja.
Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya gargadi masu rike da mukaman siyasa da su tabbatar biyayyarsu na ga gwamnatinsa ko kuma su rasa mukamansu.
An zargi ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Ezenwo Wike, da kitsa kisan marigayi Bako Angbashim, DPO na karamar hukumar Ahoada ta Gabas.
Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio ya ce likitocinsa sun tabbatar da cewar yana dauke da zazzabin cizon sauro bayan bikin cikarsa shekaru 61.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari