Yanzun Nan: FG Ta Tabbatar da Barkewa Wata Muguwar Cuta a Jihar Arewa

Yanzun Nan: FG Ta Tabbatar da Barkewa Wata Muguwar Cuta a Jihar Arewa

  • Hukumar NCDC ta ce an tabbatar da samun mutum 13 da ke dauke da muguwar cutar nan ta zazzabin Dengue a jihar Sokoto, yankin arewa maso yamma
  • A wata sanarwa da ta fitar a shafinta na yanar gizo, NCDC ta bayyana cewa an gano barkewar cutar ne a watan Nuwamba
  • Legit Hausa ta rahoto cewa NCDC ta sha alwashin inganta shirye-shiryenta a yayin da annobar cutar ta bulla

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Sokoto, jihar Sokoto - Hukumar NCDC mai yaki da cutuka masu yaduwa a Najeriya ta tabbatar da bullar cutar zazzabin Dangue a jihar Sokoto a ranar Asabar, 16 ga watan Disamba.

A cikin wata sanarwa da ta fitar a shafinta na yanar gizo, NCDC ta ce an gano bullar cutar ne a watan Nuwamban 2023.

Kara karanta wannan

Tudun Biri: Manyan malamai sun dira hedkwatar tsaro ta kasa yayin da CDS ya dauki sabon alkawari

Cutar Dengue ta bulla a jihar Sokoto
Yanzun Nan: FG Ta Tabbatar da Barkewa Wata Muguwar Cuta a Jihar Arewa Hoto: Dragana991
Asali: Getty Images

Sanarwar dauke da sa hannun Darakta Janar na NCDC, Ifedayo Adetifa, ta bayyana cewa zuwa yanzu, akwai mutum 71 da ake zargin suna dauke da ita, an tabbatar da 13, kuma ba a samu wanda ya mutu ba a jihar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Masu dauke da cutar sun fito ne daga kananan hukumomi uku - Sokoto ta Kudu (60), Wamako (uku) sai Dange Shuni (daya).

Hukumar ta ce a halin da ake ciki yanzu barazanar barkewar cutar ta dengue yana a tsaka-tsaki dangane da kimanta hadarin da ke tattare da shi.

Legit ta rahoto cewa zazzabin Dengue cuta ce mai radadi, zazzabin cizon sauro mai zafi wanda daya bisa hudu na kwayoyin Dengue ke haifar da shi. Yana iya zama mai barazana ga rai a cikin yan sa'o'i kadan kuma sau da yawa yana bukatar kulawa a asibiti.

Kara karanta wannan

Gobara ta babbake ofisoshi akalla 17 a sakateriyar ƙaramar hukuma 1 a jihar Kano

Kwalara ta bulla a jihar Ogun

A wani labari na daban, mun ji cewa gwamnatin jihar Ogun ta ankarar da mutane kan bullar cutar Kwalara a karamar hukumar Ijebu ta Arewa a jihar.

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da hadimirsa a harkar lafiya, Dakta Tomi Coker ta fitar a yau Lahadi 17 ga watan Satumba.

Coker ta bayyana Kwalara a matsayin cutar da ke yaduwa a lokacin damuna da kuma rashin tsafta na muhalli, Vanguard ta tattaro.

Asali: Legit.ng

Online view pixel