Bayan Rasa Mukamin Minista El-Rufa'i Ya Samu Mukamin Sarauta

Bayan Rasa Mukamin Minista El-Rufa'i Ya Samu Mukamin Sarauta

  • Awujale na Ijebuland zai karrama Mallam Nasir Ahmad El-Rufai, tsohon gwamnan jihar Kaduna
  • Za a karrama El-Rufai da sarauta a ranar Asabar, 16 ga watan Disamba, a matsayin Gbobaniyi na Ijebuland
  • Wannan nasarar ta sanya shi zama ɗan Arewa na farko da aka ba shi muƙami a tarihin Ijebuland

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Ijebu Ode, Ogun - Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasir El-Rufai, na gab da samun sarautar Gbobaniyi na Ijebuland a jihar Ogun.

El-Rufai ya sanar da hakan ne a shafinsa na X a ranar Juma’a, 15 ga watan Disamba.

El-Rufai ya samu sarauta
Za a nada El-Rufai sarautar Gbobaniyi na Ijebu Hoto: Nasir El-Rufai
Asali: Facebook

Wannan sabuwar nasarar da ya samu ta sanya shi ya zama na farko wanda ba Bayerabe ba, ɗan Arewa, ko wanda ba ɗan yankin Kudu maso Yamma da aka ba shi sarauta a Ijebuland.

Kara karanta wannan

Babban hafsan tsaro CDS ya faɗi matakin da suka ɗauka kan sojojin da suka kashe Musulmai a Kaduna

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mai Martaba Sarki Oba Sikiru Kayode Adetona, wanda shi ne babban mai mulki kuma Awujale na Ijebuland ne zai ba El-Rufai muƙamin sarauta.

Cikin jin dadin wannan labari, El-Rufai a shafinsa na X, ya rubuta:

"Har ila yau, na ji daɗin zama ɗan Najeriya na farko wanda ba ɗan yankin Kudu maso Yammacin Najeriya ba da Awujale ya ba ni sarauta a shekaru kusan 64 da ya yi yana mulki."
"Za a bani sarautar Gbobaniyi na Ijebuland. Ina godiya ga Kabiyesi Awujale da ya karrama ni kuma ina godiya ga duk waɗanda suka yi min fatan alheri."

Awajule zai karrama Otunba Lawal da muƙaman sarauta biyu

Hakazalika, tsohon ɗan takarar gwamna a jam’iyyar PDP a jihar Ogun, Otunba Jimi Lawal, za a ba shi sarautu biyu.

Kamar yadda El-Rufai ya wallafa a shafinsa na X, za a karrama Otunba Lawal ne saboda gudunmawar da ya bayar a masarautar Ijebu da Najeriya, tare da matarsa, Maryam Lawal.

Kara karanta wannan

Wata Sabuwa: Ana zargin Shugaba Tinubu da rura wutar rikici a jihar PDP, bayani sun fito

El-Rufai ya rubuta:

"Don Allah ku taya ni da Jimi da ƴan uwa da abokan arziki addu’o’in Allah ya sa a yi taro lafiya, da tsawon rai da lafiya ga mai martaba Awujale da mu baki daya."

El-Rufai Ya Ziyarci Babangida

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasir Ahmad El-Rufai ya ziyarci tsohon shugaban ƙasa Ibrahim Badamasi Babangida.

El-Rufai ya ziyarci tsohon shugaban ƙasa Babangida ne kwanaki kaɗan bayan ya kai irin wannan ziyarar a Daura wajen tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng