Yan Bindiga Sun Bi Basarake Har Fadarsa Sun Dauki Ransa a Arewacin Najeriya

Yan Bindiga Sun Bi Basarake Har Fadarsa Sun Dauki Ransa a Arewacin Najeriya

  • Yan bindiga sun kai kazamin gari fadar hakimin garin Sarkin Kudu da ke karamar hukumar Ibbi ta jihar Taraba
  • Maharan sun yi ajalin hakimin na Sarkin Kudu mai suna Ali Hakimi, a daren ranar Juma'a, 15 ga watan Disamba
  • Zuwa yanzu ba a samu jin ta bakin rundunar yan sandan jihar ba, domin kakakinta, SP Usman Abdullahi bai dauki waya ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Jihar Taraba - Tsagerun yan bindiga sun kashe hakimin garin Sarkin Kudu da ke karamar hukumar Ibbi ta jihar Taraba.

Kamar yadda jaridar Daily Trust ta rahoto, maharan sun farmaki hakimin, Ali Hakimi, a cikin fadarsa da ke garin Sarkin Kudu da misalin karfe 12:30 na daren ranar Juma'a, 15 ga watan Disamba.

Kara karanta wannan

Tudun Biri: Kwankwaso ya kai ziyarar jaje game da harin bam a Kaduna, ya tura muhimmin sako

Yan bindiga sun halaka hakimin Sarkin Kudu
Yan Bindiga Sun Bi Hakimi Har Fadarsa Sun Dauki Ransa a Arewacin Najeriya Hoto: Nigeria Police Force
Asali: Facebook

Wata majiya a yankin ta sanar da jaridar cewa yan bindigar, kimanin su 10 sun shiga fadar hakimin ta karfi da yaji sannan suka harbe shi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wani mai suna Bello Adamu ya fada ma jaridar cewa marigayin shine kanin sarkin masarautar Sarkin Kudu.

Ya ce a yan baya-bayan nan, tsagerun yan bindigar sun kai hare-hare da dama a fadin masarautar sannan sun yi awon gaba da mutane da dama.

Majiyar ta ce:

"Maharan sun tsere cikin jeji bayan kashe hakimin kuma kowa a yankin yana cikin tsoro saboda babu wanda ya san wanda yan bindigar za su kai wa hari nan gaba."

Sai dai ba a samu jin ta bakin kakakin yan sanda a jihar, SP Usman Abdullahi, ba kan al'amarin domin wayarsa a kashe take lokacin da aka kira shi.

Kara karanta wannan

Tudun Biri: Manyan malamai sun dira hedkwatar tsaro ta kasa yayin da CDS ya dauki sabon alkawari

Yan bindiga sun farmaki Zamfara

A wani labarin kuma, mun ji cewa wasu miyagun ƴan bindiga sun kai sabon hari kan mazauna garin Zurmi, hedkwatar ƙaramar hukumar Zurmi a jihar Zamfara.

Kamar yadda Channels tv ta ruwaito, yayin harin ƴan bindigan sun yi awon gaba da mutane aƙalla 10 zuwa cikin daji.

An ce maharan sun kutsa kai cikin garin Zurmi da yammacin jiya Talata kuma daga zuwa suka buɗe wuta kan mai uwa da wabi, lamarin da ya tilasta ma jama'a gudun neman tsira.

Asali: Legit.ng

Online view pixel