Manyan Labarai A Yau
Kungiyoyin kwadago sun yi barazanar shiga yajin aiki idan gwamnatin tarayya da jihohi suka ki biyan karin albashi da alawus na ma'aikata da aka alkawarta.
Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu ya amince da karin N35,000 a albashin ma'aikatan gwamnatin jihar, da alawus na kashi 50% na albashin Disamba.
A wata hira, Eunice Atuejide ta bayyana cewa duk hukuncin da Kotun Koli za ta yanke sabanin abun da mutane ke so, wanda shine Abba zai haifar da tashin hankali.
Miyagun yan bindiga sun kai sabon farmaki a Katsina inda suka halaka manoma mutum hudu. An nemi wasu mutane masu yawa an rasa bayan harin yan bindigan.
Tsohon shugaban jam’iyyar APC na kasa, Alhaji Abdullahi Adamu, ya sanar da yin ritaya daga siyasa. Adamu ya bayyana cewa baya sha’awar siyasa a yanzu.
Ana tsaka da rikicinsa da Gwamna Siminalayi Fubara, Wike ya dira birnin Port Harcourt tare da tawaga mai tarin yawa domin yin wani muhimmin abu a jihar.
Wani shugaba a yankin Neja-Delta ya bayyana cewa a yayin da ake tsaka da rikiciɓtsakanin Gwamna Fubara da Nyesom Wike, gwamnan ya so ya hakura da mulki.
Gabannin yanke hukunci, Sarakunan Hausawa a Kudu maso Yamma sun gargadi shugabannin siyasa da kada su cinnawa Najeriya wuta saboda zaben gwamnan jihar Kano.
Shugaban cocin RCCG, Fasto Enoch Adeboye ya yi maganganu masu dadi a kan Najeriya. Malamin addinin ya ce duk da wahalar da ake ciki, makomar Najeriya na da girma.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari