Abba vs Gawuna: Jigon LP Ta Bayyana Wanda Ya Kamata Kotun Koli Ta Ayyana a Matsayin Gwamnan Kano

Abba vs Gawuna: Jigon LP Ta Bayyana Wanda Ya Kamata Kotun Koli Ta Ayyana a Matsayin Gwamnan Kano

  • Hukuncin Kotun Koli kan rikicin zaben gwamnan Kano shine zai tabbatar da ainahin wanda ya lashe zaben ranar 18 ga watan Maris a jihar
  • Ana shari'a ne tsakanin Gwamna Abba Kabir Yusuf na NNPP da Nasiru Yusuf Gawuna na APC, wanda kotun daukaka kara ta ayyana a matsayin wanda ya lashe zabe
  • Gabannin yanke hukuncin, wata mai nazarin harkokin siyasa kuma jigon jam'iyyar LP, Eunice Atuejide, ta bayyana cewa Abba ne zabin mutane kuma shi ya kamata a ba nasara

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Jihar Kano - Eunice Atuejide, yar takarar jam'iyyar Labour Party (LP) na mazabar Apapa a zaben 2023, ta bukaci Kotun Koli da ta yanke hukunci da zai ba Gwamna Abba Kabir Yusuf na jam'iyyar NNPP nasara.

Kara karanta wannan

Tsige Gwamna Mutfwang na Filato: APC ta fadi wanda zai yi nasara a Kotun Koli

A wata hira ta musamman da ta yi da Legit Hausa a ranar Asabar, 16 ga watan Disamba, Atuejide ta jaddada cewar ya kamata muradin mutane ya yi tasiri a hukuncin karshe da Kotun Koli za ta yanke kan takaddamar zaben gwamnan jihar Kano.

Jigon LP ta ce Abba ne zabin al'ummar Kano
Abba vs Gawuna: Jigon LP Ta Bayyana Wanda Ya Kamata Kotun Koli Ta Ayyana a Matsayin Gwamnan Kano Hoto: Abba Kabir Yusuf, Eunice Atuejide, GawunaOnline
Asali: Facebook

Ku tuna cewa kotun daukaka kara a Abuja ta tsige Gwamna Yusuf a ranar 17 ga watan Nuwamba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kotun ta tabbatar da hukuncin kotun zabe karkashin jagorancin Mai shari'a Oluyemi Akintan Osadebay, wacce ta tsige Yusuf a ranar 20 ga watan Satumba, 2023.

Karamar kotun ta ayyana Nasiru Gawuna na APC a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Kano na ranar 18 ga watan Maris, inda Gwamna Yusuf ya garzaya Kotun Koli don kalubalantar tsige shi da aka yi.

Da take ci gaba da magana, tsohuwar yar takarar shugaban kasa, Atuejide, ta yi gargadin cewa duk wani hukunci da zai saba zabin mutane na iya haddasa tashin hankali a Kano da sauran jihohi a fadin kasar.

Kara karanta wannan

Abba vs Gawuna: Kada ku cinnawa Najeriya wuta saboda zaben gwamnan Kano - Shugabannin Hausawa a kudu

Jigon ta LP ta ce:

"Ya kamata Kotun Koli ta yanke hukunci da zai kai nasara wajen dan takarar NNPP Abba Kabir Yusuf saboda shine gwamnan da mutanen Kano suka zaba.
"Shakka babu duk wani abu na daban,zai haifar da mummunan tashin hankali a Kano wanda tabbas zai iya gangarawa zuwa sauran jihohin kasar."

Legit Hausa ta nemi jin ta bakin wata mazauniyar Kano game da hukuncin da suke tsammani daga Kotun Koli inda suka nuna lallai Abba take so ya samu nasara.

Malama Ummi Zainab ta ce:

“Ai ba ni kadai ba duk wani mai kishin Kano Abba yake so ya ci gaba da kasancewa kan mulki, kuma kowa ma ya san Abba ne ya ci zabe. Ina mai kira ga Kotun Koli da ta sanya ra’ayin mutane a sama da na kowa.
“Abba shine zabinmu mu Kanawa kuma shine ya ci zabe kokarin murde masa kujerarsa daidai yake da jefa mu cikin halin wayyo Allah. Don Allah alkalan Kotun Koli su yi mana adalci, sune madogara na karshe da muke da shi. Allah ya ci gaba da zaunar da mu lafiya.”

Kara karanta wannan

"Ainahin dalilin da yasa muka tsige gwamna da yan majalisar PDP 16": Alkalin kotun daukaka kara

Filato: Jigon APC ya yi hasashen mai nasara

A wani labarin kuma, mun ji cewa wani mai nazari kan harkokin siyasa kuma jigon jam'iyyar APC, Williams Dakwom, ya jero manyan abubuwan da ka iya yin tasiri kan jam'iyyar PDP reshen jihar Filato a shari'ar da ke gudana a Kotun Koli.

A wata hira ta musamman da jaridar Legit a ranar Asabar, 16 ga watan Disamba, ta wayar tarho, Dakwom ya jaddada cewa umurnin kotun na neman PDP ta gudanar da tarukanta, wanda suka saba, na iya tasiri a hukuncin karshe da Kotun Allah ya isa za ta yanke.

Asali: Legit.ng

Online view pixel