Tsohon Shugaban APC Na Kasa, Abdullahi Adamu Ya Yi Ritaya Daga Siyasa

Tsohon Shugaban APC Na Kasa, Abdullahi Adamu Ya Yi Ritaya Daga Siyasa

  • Tsohon shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Adamu ya bayyana matsayinsa a harkokin siyasa a yanzu
  • Adamu ya bayyana cewa ya yi ritaya daga harkokin siyasa tare da daina magana kan abun da ya shafi bangaren
  • Tsohon gwamnan na jihar Nasarawa ya ce kwatakwata ya daina sha’awar duk wani abu da ya shafi siyasa

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

FCT, Abuja - Tsohon shugaban jam'iyyar APC na kasa, Sanata Abdullahi Adamu, ya bayyana cewa ya yanke shawarar ficewa daga harkokin siyasa.

Kamar yadda jaridar Daily Trust ta rahoto a ranar Asabar, 16 ga watan Disamba, Adamu ya bayyana cewa ayyukan siyasa sun fara hawa masa kai.

Abdullahi Adamu ya yi ritaya daga siyasa
Yanzun Nan: Tsohon Shugaban APC Na Kasa, Abdullahi Adamu Ya Yi Ritaya Daga Siyasa Hoto: @OfficialAPCNg
Asali: Twitter

Adamu ya bayyana hakan ne a wajen kaddamar da wani littafi na nasarorin da Gwamna Abdullahi Sule ya samu a jihar Nasarawa daga 2019 zuwa 2023 wanda Abdullahi Tanimu ya wallafa.

Kara karanta wannan

An kama wani mutum bayan ya ziyarci surukansa ba tare da sadaki ba, sun dafa abinci da komai na biki

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'Na daina magana kan siyasa', Abdullahi Adamu

Da yake jawabi, tsohon shugaban na APC, wanda ya kasance gwamnan farar hula na farko a jihar, ya yi mulki tsakanin 1999 da 2007, ya yabawa mawallafin littafin kan kokarinsa na jero nasarorin gwamnan.

Ya ce gwamnan ya karfafa nasarorin da magabatansa suka samu tare da inganta su, yayin da ya shawarci masu ruwa da tsaki da al’ummar jihar da su ci gaba da yi wa gwamna da yan majalisarsa addu’a don su samu damar kai jihar zuwa ga mataki mai girma.

Jaridar Daily Post ta rahoto cewa Adamu, wanda ya kaddamar da kwafin littafin 20 kan naira miliyan daya, ya bayyana cewa:

"Ba wai ritaya kawai zan yi ba illa zan fita daga siyasa. Na fara dan kyankyamin ayyukan siyasa da maganganun siyasa a yanzu. Don haka ku yafe min, ba zan yi wata magana ta siyasa da ta wuce neman karin goyon baya ga gwamnan jihar ba.

Kara karanta wannan

Tudun Biri: Manyan malamai sun dira hedkwatar tsaro ta kasa yayin da CDS ya dauki sabon alkawari

"Yana bukatar dukkan addu'o'in ku da fatan alheri don samun nasara."

Jerin yan siyasa 4 da suka rabu da Wike

A wani labari na daban, mun ji cewa jihar Ribas na fama da rikicin siyasa tun a karshen watan Oktoba lokacin da wasu yan majalisa suka yi kokarin tsige Gwamna Siminalayi Fubara.

Ana ganin yan majalisar da suka yi yunkurin tsige gwamnan sun yi hakan ne bisa umurnin Nyesom Wike, ministan babban birnin tarayya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel