Yar Najeriya Ta Gina Dankareren Gida a Wata 7, Ta Yi Bidiyo Ta Na Tikar Rawa Don Murna

Yar Najeriya Ta Gina Dankareren Gida a Wata 7, Ta Yi Bidiyo Ta Na Tikar Rawa Don Murna

  • Wata ‘yar Najeriya da ta gina gidan ta a cikin wata bakwai kacal ta burge mutane da dama a yanar gizo
  • Ta wallafa bidiyo na katafaren ginin, wanda ke da kyakkyawan tsari da fenti mai sheki da ya ja hankalin jama'a
  • Bidiyon ya nuna matar a tsaye kusa da gidan, tana nuna farin cikinta da rawa cikin jin dadin gina wannan dakareren gida

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Wata mata 'yar Najeriya ta baiwa mutane da dama mamaki a yanar gizo bayan nuna gagarumar nasarar da ta samu na gina gidanta a cikin wata bakwai kacal.

Ta wallafa bidiyo na ginin mai ban sha'awa, wanda ke da tsari na zamani da fenti mai sheki wanda ke daukar haske.

Kara karanta wannan

Mijin Hajiya: Bidiyon mutumin da ya goyi dansa suka shiga kasuwa ya jawo cece-kuce a duniya

Yar Najeriya ta gina gidanta a wata 7
Yar Najeriya ta baiwa mutane da dama mamaki bayan nuna gidan da ta gina a cikin wata 7 kacal. Hoto: @mhizvickyblizz/TikTok
Asali: TikTok

Bidiyon gidan da ta gina a wata bakwai

Bidiyon ya nuna ta a tsaye a kusa da gidan cike da alfahari, tana nuna farin cikinta tare da yin rawa ta ban sha'awa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jama’a da dama sun taya ta murna tare da yaba mata kan kwazonta da jajircewa.

Kalli bidiyon a kasa:

Budurwa ta wallafa bidiyon hamshakan masu kudi 150

A wani labarin, Legit Hausa ta kawo maku rahoton wata budurwa da ta wallafa bidiyon sunayen wasu attajiran samari 150 da ke neman matan aure ruwa a jallo.

Budurwar ta yi wa jerin sunayen take da "jerin sunayen Malak", sannan ta wallafa shi a shafinta na TikTok da yakinin zai taimaka wa mata wajen haduwa da mijin aure.

Duk da cewa jerin sunayen na dauke da sunayen maza 'yan kasar Masar ne kawai, sai da budurwar ta ce ita ma a can kasar ta hadu da nata abokin rayuwar.

Kara karanta wannan

"Shugaba a shekaru 20": Yar Najeriya ta yi tattalin kudinta da kyau, ta gina hadadden gidan dinki

Sarauniyar kyau ta duniya ta angwance da attajirin mai kudi daga Najeriya

A wani labarin kuma, Mitchel Ihezue, sarauniyar kyau ta duniya daga Najeriya ta shirya angwancewa da hamshakin dan kasuwa kuma dan siyasa, Yarima Ukachwukwu, rahoton Legit Hausa.

Rahoton ya bayyana cewa, Mitchel na da shekaru 26 a duniya yayin da saurayin nata Yarima Nicholas Ukachukwu ke da shekaru 57 a duniya.

Ikukuoma ya kasance hamshakin dan kasuwa wanda ke da 'ya'ya biyar, kuma ya rasa matarshi shekaru uku da suka gabata.

Asali: Legit.ng

Online view pixel