Manyan Labarai A Yau
Wasu miyagun yan bindiga sun sake kai sabon hari a jihar Zamfara. Yan bindigan sun kutsa har cikin gida sun yi awon gaba da basarake da babban limami.
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da murabus din Simon Lalong, mimistan kwadago da samar da ayyukan yi. Majiya daga fadar shugaban kasa ta tabbatar.
Rahotanni daga fadar shugaban kasa sun nuna cewa Bola Ahmed Tinubu na tattaunawa da wakilan ƙungiyar gidajen jaridu ta ƙasa NPAN a fadarsa Villa Abuja.
Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour Party (LP), Peter Obi, ya zargi gwamnatin Tinubu da yi masa barazana domin hana shi sukar da yake yi.
An samu wani mutumi da ya addabi wata mata a kan hanya ko ta iya yin kunu. Nan take wannan Baiwar Allah ta shigar da kara a gaban 'yan sanda, yanzu yana hannu.
An samu asarar rayukan mutum biyu bayan wani mummunan hatsarin mota ya ritsa da su a jihar Ogun. Wasu daga cikin wadanda hatsarin ya ritsa da su sun samu raunuka.
Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya shirya gina asibiti ko makarantar Islamiyya domin tunawa da Asma'u Sani wacce ciwon kansa ya halaka a Kano.
Jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a jihar Rivers ta sake nanata cewa kujerun yan majalisar da suka sauya sheka zuwa APC, har yanzu babu kowa a kansu.
Wata yar Najeriya ta samu babbar kyauta inda ta haifi yara biyar a lokaci daya. Matar ta garzaya TikTok inda ta nuna katoton cikinta da yaran da ta haifa.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari