Gwamna Abba Kabir Zai Yi Wani Muhimmin Abu 1 Domin Tunawa da Asma'u Sani Wacce Kansa ta Kashe
- Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya kai ziyarar ta'aziyya a gidansu Asma'u Sani wacce ta rasu saboda ciwon kansa
- Gwamnan ya yi alƙawarin gina asibiti ko makarantar Islamiyya domin tunawa da marigayiya Asma'u Sani
- Kuɗin da gwamnan ya ware domin ɗaukar nauyin zuwa da ita Indiya domin yi mata tiyata, za a kai iyayenta aikin Umrah da su
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kano - Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya yi alƙawarin gina asibiti ko makarantar Islamiyya domin tunawa da marigayiya Asma’u Sani, wacce ta rasu kafin ta tafi ƙasar Indiya yi mata tiyata.
Gwamna Yusuf ya ɗauki nauyin yi wa Asma'u aikin tiyata a Indiya, amma ta rasu kafin zuwan ranar da za su tafi zuwa asibiti a Indiya.
Hakan na ƙunshe a cikin sanarwar da daraktan wayar da kan jama’a na gidan gwamnati, Aliyu Yusuf ya fitar a ranar Lahadi, 17 ga watan Disamba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamna Abba ya je ta'aziyya
Sanarwar ta yi nuni da cewa Gwamna Yusuf ya yi wannan alƙawarin ne tare da mataimakinsa, Aminu Abdulsalam Gwarzo, a wata ziyarar ta’aziyyar da suka kai gidansu marigayiyar da ke unguwar Alkalawa a ƙaramar hukumar Gwarzo.
Sanarwar ta ƙara da cewa:
"Gwamnan, wanda ya yi matuƙar alhinin rasuwar Asma’u, ya bayyana rasuwar a matsayin abin ban tsoro da ban tausayi, yana mai addu’ar Allah ya jiƙanta da rahama ya kuma baiwa ƴan uwa hakurin jure wannan babban rashi."
"Gwamna Yusuf ya umurci Limamin yankin da ya samar da fili don gina asibiti ko makarantar Islamiyya, wanda za a sanyawa sunan Asma’u."
"Ya kuma ba da umarnin cewa, kuɗin da aka ware domin jinyar marigayiyar, za a yi amfani da su ne domin kai iyayenta zuwa kasa mai tsarki domin gudanar da aikin Umrah."
Wacce addu'a iyayen Asma'u suka yi?
Mahaifin marigayiyar, Malam Sani wanda ya ji dadin karramawar da gwamnan ya yi musu, ya roƙi Allah maɗaukakin Sarki da ya tabbatar da zaɓen gwamnan a kotun ƙoli, ya kuma saka masa da Al-Jannatul Firdausi.
Gwamna Yusuf ya haɗu da Asma’u ne a lokacin da ya kai ziyarar duba marasa lafiya asibitin kashi na Dala inda ya samu labarin halin da take ciki.
Gwamna Abba Zai Biya Kuɗin Diyya
A wani labarin kuma, kun ji cewa daga ƙarshe Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya sadudu zai biya kuɗin diyyar rusau da ya yi a Kano.
Gwamnan ya amince da biyan naira biliyan uku don diyyar rusau na shagunan masallacin Idi da kungiyar ƴan kasuwa.
Asali: Legit.ng