Gwamna Bago Ya Haramta Sanya Atampa, Babbar Riga Da Kaftani Zuwa Wajen Aiki

Gwamna Bago Ya Haramta Sanya Atampa, Babbar Riga Da Kaftani Zuwa Wajen Aiki

  • Gwamna Umar Bago na jihar Neja ya bayar da sabon umurni ga ma'aikatan gwamnati a jiharsa
  • Daga yanzu, gwamnan ya umurci ma'aikata da su daina sanya manyan kaya kamar su Babbanriga, kaftani da sauransu zuwa wajen aiki
  • A cewarsa, za a kori duk wanda ya tsallake wannan umurni daga bakin aiki, kuma suna iya saka kayan a ranar Juma'a kawai

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Jihar Niger - Gwamnan jihar Neja, Umar Bago, ya haramtawa ma'aikatan gwamnati sanya tufafin gargajiya zuwa ofis a jihar.

Bago wanda ya yi magana a ranar Litinin, 18 ga watan Disamba, yayin gabatar da kayan raya kasa da tsare-tsare a kamfanin Brains and Hammers Rice City da ke karamar hukumar Wushishi ta jihar.

Kara karanta wannan

Waiwayen shekara: Jerin yan siyasar Najeriya mafi shahara a 2023

Bago ya haramta wa ma'aikata sanya manyan kaya zuwa wajen aiki
Gwamnan Arewa Ya Haramta Sanya Atampa, Babbanriga da Manyan Kaya Zuwa Wajen Aiki Hoto: Gov. Mohammed Umaru Bago
Asali: Facebook

Ya ce kada a dunga sanya tufafin gargajiya kamar su "babbanriga da dogayen kaya irin su kaftani" zuwa ofis daga Litinin zuwa Alhamis, rahoton The Cable.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Duk wanda ke sha'awar manyan kaya ya ajiye aiki - Bago ga ma'aikatan gwamnati

A cewar gwamnan, ya zama dole gaba daya ma'aikatan gwamnati su bi wannan umurni, yana mai cewa za a sallami duk wanda ya ketare wannan umurni daga aiki.

Gwamnan ya ce gwamnatinsa ta mayar da hankali wajen yi wa jihar hidima, yana mai cewa duk wanda ke burin sanya tufafin gargajiya to ya yi murabus daga aiki.

Ya ce an yi wa ma'aikatan gwamnati izinin yi shiga irin ta Turawa ne kawai a ranakun aiki, yana mai cewa suna iya sanya kayan gargajiya a ranakun Juma'a.

Bago ya ce:

"Daga ranar Litinin, za mu kafa doka da zai hana ma'aikatan gwamnati sanya dogayen kaya da babbanriga zuwa wajen aiki tsakanin Litinin da Alhamis. Babu Babbanriga, babu dogayen kaya, aiki muka zo yi a nan.

Kara karanta wannan

Bikin Kirsimeti: Gwamnan APC ya ba ma'aikata hutun kwanaki 14

"Duk wanda ke son sanya Babbanriga ya yi murabus. Za kuma mu shiga harkar noma gadan-gadan don ci gaba."

Gwamnatin Neja za ta dukufa harkar noma

Gwamnan ya kuma ce dole ne matasa da ma’aikatan gwamnati da yan siyasa da masu rike da mukaman gargajiya su koma gona, rahoton Daily Post.

A cewarsa, akwai arziki a harkar noma, inda ya jaddada matsayinsa na baya cewa jihar ba ta da wani dalilin da zai sa ta zama matalauciya da dimbin filayen noma.

Bago ya yi amfani da dandalin ne wajen karfafa wa matasa gwiwa kan harkokin noma, inda ya ce gwamnati za ta fara rabawa mata da matasa 250,000 kowannensu domin saukaka ayyukan noma.

Legit Hausa ta zanta da wani dan jihar Neja don jin ta bakinsa game da wannan sabon umurni da gwamnan ya bayar.

Malam Ndanitsa ya ce:

“Wannan zance ne ma mara amfani. Shin abun da al’umma ke bukata kenan? Menene hadin gwamna da irin tufafin da ma’aikata ke sanyawa? Kawai abun da al’umma ke bukata shine kawo sauyi musamman kan lamarin tsaro babu ruwan mu da maganar tufafin ma’aikata.

Kara karanta wannan

Gwamna Bago ya hana ma'aikata sanya babban riga da kaftani? Gaskiya ta bayyana

“Toh har nawa ne ma albashin da za a kara masu nauyin siyan wasu tufafi da sunan aiki. Ya kamata gwamnan ya mayar da hankali kan ayyukansa kada ya bari shirme ya dauke masa hankali.”

Bago ya hana hijabi a Neja?

A baya mun ji cewa gwamnan jihar Neja, Mohammed Bago, na jam'iyyar APC ya ce jihar ba ta adawa da sanya hijabi da mata musulmai ke yi.

Bago yana mayar da martani ne kan wani rahoto da aka wallafa a kafafen sada zumunta na yanar gizo da ke iƙirarin cewa kwamishiniyar ilimi ta jihar, Hajiya Hadiza, ta yi Allah-wadai da sanya Hijabi da malamai mata ke yi, cewar rahoton Punch.

Asali: Legit.ng

Online view pixel