Direban Tasi Ya Tsinci Jakar Kudi a Motarsa, Bidiyo Ya Bayyana Yayin da Ya Mayar da Shi

Direban Tasi Ya Tsinci Jakar Kudi a Motarsa, Bidiyo Ya Bayyana Yayin da Ya Mayar da Shi

  • Bandir-bandir din kudi da wani direban tasi ya tsinta a motarsa ya bar masu amfani da soshiyal midiya cikin kaduwa kuma ya hadda cece-kuce
  • Kamar yadda rahotanni suka kawo, wani mai halartan taro a Port Harcourt ne ya manta da kudin a cikin tasi din mutumin
  • Yayin da mutane da dama suka yaba gaskiya da amanar mai tasi din, wasu sun yi watsi da abun da ya aikata

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Wani direban tasi da ba a bayyana sunansa ba ya haddasa cece-kuce a soshiyal midiya bayan ya mayar da bandir-bandir na kudi da wani fasinja ya manta a motarsa.

Portharcourt Specials, wanda ya kawo rahoton ya saki wani bidiyo da ke nuna yadda mutanen biyu suka bude bakar jakar sannan suka fitar da bandir-bandir na kudi.

Kara karanta wannan

Babban hafsan tsaro CDS ya faɗi halin da ake ciki a bincike kan jefa Bam a taron Musulmai a Kaduna

Direban tasi ya tsinci jakar kudi a motarsa
Direban Tasi Ya Tsinci Jaka da Makudan Kudi a Motarsa, Bidiyo Ya Bayyana Yayin da Ya Mayar da Shi Hoto: Luca Sage, Facebook/Portharcourt Specials
Asali: Getty Images

Kamar yadda kafar labaran ta Facebook ta bayyana, wani mai halartan taro a Port Harcourt ne ya manta kudin. An rahoto cewa direban ya mayar da makudan kudin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gaskiyar direban ya sa janyo masa farin jini a wajen masu amfani da soshiyal midiya da dama, amma sam bai burge wasu ba.

A ganinsu, direban bai da zabi ne domin bayanansa na nan a manhajar kamfanin da yake aiki.

Jama'a sun yi martani kan gaskiyar mutumin

Roy Owhorndah ya ce:

"A yadda kasar nan take a yanzu mutum yake manta irin wannan kudi me mutumin yake tunani?"

Wilson Chukwuyem ya ce:

"Dalilin da yasa yake da kyau mutum ya dunga amfani da tasi na kamfani, idan ba don haka ba da mutumin ba zai dawo da kudin ba."

Fâbîân Zâddy Ûdô ya ce:

Kara karanta wannan

Tsaka mai wuya: Sama da 'yan Najeriya 1,000 aka damfara da sunan sama masu aiki a Burtaniya

"Ya ji tsoro cewa za a yi karar motarsa don haka ya mayar da kudin.
"Mayaudari."

Etonex Obo ya ce:

"Ya yi kyau.
"Koda ni ne abun da zan yi kenan.
"Zama mutum nagari ko bata gari ra'ayi ne."

Young Chinda ta ce:

"Wannan abun a baya ne! Ba kodayaushe mu dunga ji da kawo rahoton abu mara kyau game da jihar Ribas ba."

Direban adaidaita ya tsinci kudi

A wani labari makamancin wannan, mun ji cewa an karrama wani mai adaidaita sahu, Ali Bulama a kauyen Jumbam, karamar hukumar Tarmuwa da ke jihar Yobe, bayan ya tsici kudi tare da mayarwa.

An kuma yi wa Bulama kyautar kudi N100,000 bayan ya mayarwa fasinja da miliyan tara da ya mata a kekensa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel