Manyan Labarai A Yau
Jami'an hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi (NDLEA) sun yi nasarar kama wata mata yar shekara 70 da jikanta a Legas kan zargin sayar da miyagun kwayoyi.
Fitaccen faston Najeriya, Primate Elijah Ayodele ya bayyana cewa farashin shinkafa yar waje zai kai N80,000 kan kowani buhu a cikin shekarar 2024.
An samu aukuwar wani mummunan hatsarin mota a jihar Jigawa. Hatsarin motar ya yi sanadiyyar salwantar da rayukan fasinjoji mutum 11 da ya ritsa da su.
Rahotanni sun nuna cewa wani dan sanda ya bindige jarumin fina-finan Najeriya, Azeez Olalade Ijaduade, a jihar Ogun. Jarumin na can kwance cikin mawuyacin hali.
Gwamnatin tarayya na duba yiwuwar sake siyan wasu bankunan kasuwanci guda biyu da aka siyar a lokacin tsohon gwamnan babban bankin Najeriya, Godwin Emefiele.
Rundunar yan sandan Najeriya ta yi magana kan harbin da wani jami'in dan sanda ya yi wa jarumin fina-finan Najeriya Azeez Ijaduade. Ta ce ana gudanar da bincike.
Tsohuwar ministar man fetur a zamanin mulkin tsohon Shugaba Goodluck Joɓathan, Diezani Alison Madueke, ta musanta yin hira inda ta zargi gwamnan Zamfara.
Wata babbar fasto a majami’ar Transformation World Ministries, Francisca Emmanuel, ta ce yana cikin littafi mutum ya zama matsafi maimakon dukufa ga addu’a.
Tsohon gwamnan jihar Sokoto, Attahiru Bafarawa, ya yi magana kan batun bukatar Shugaba Tinubu ya binciki gwamnatin tsohon Shugaba Muhammadu Buhari.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari