Buhun Shinkafa Zai Koma N80,000, Za a Yankewa Wasu Sanatoci Daurin Rai-Da-Rai a 2024, Malamin Addini

Buhun Shinkafa Zai Koma N80,000, Za a Yankewa Wasu Sanatoci Daurin Rai-Da-Rai a 2024, Malamin Addini

  • Fitaccen faston Najeriya, Primate Babatunde Elijah Ayodele ya hango abubuwan da ke tunkaro Najeriya a 2024
  • A hasashensa na sabuwar shekara, malamin addinin ya ce buhun shinkafa yar waje zai kai N80,000 a shekara mai zuwa
  • Haka kuma, Ayodele ya ce wasu sanatocin kasar za su fuskanci daurin rai da rai

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Kamar yadda ya saba bisa al'ada, shugaban cocin INRI Spiritual, Primate Babatunde Elijah Ayodele (JP), ya saki sakonninsa game da shekarar 2024.

A hasashensa, malamin addinin ya bayyana cewa farashin shinkafa yar waje zai yi tashin gwauron zabi uwa N80,000 kan kowani buhu daya a kasar.

Primate Primate Elija Ayodele ya yi hasashen tsadar shinkafa
Buhun Shinkafa Zai Koma N80,000, Za a Yankewa Wasu Sanatoci Daurin Rai-da-Rai a 2024, Malamin Addini Hoto: Primate Elija Ayodele
Asali: UGC

Haka kuma, babban faston ya yi hasashen cewa wasu sanatocin Najeriya za su fuskanci hukuncin daurin rai da rai a shekara mai zuwa.

Kara karanta wannan

Jerin hasashe 5 masu daga hankali da wani fitaccen malamin addini ya yi game da 2024

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jaridar PM News ta rahoto cewa malamin addinin ya gudanar da taronsa na manema labarai na shekara a ranar Juma'a a hedkwatar cocin INRI da ke rukunin gidaje na Prosperity, Oke-Afa, Ejigbo, Lagos inda a nan ne ya yi hasashensa game da 2024.

Hasashen na kunshe ne a takarda mai shafuka 91 wanda ya saki a ranar Juma'a, 22 ga watan Disamba, 2023.

Haka kuma, ya yi hasashen cewa farashin Dala zai tashi zuwa N1400 kuma zai girgiza tattalin arziki ba da wasa ba, rahoton Daily Post.

Ya ce:

“Tattalin Arzikin Kasar zai rika canzawa ta yadda Babban Bankin Najeriya zai koka. Tallafin Gwamnati na daga cikin abubuwan da ke lalata tattalin arziki kuma babu tasirin da ya yi wajen farfado da tattalin arziki. Shinkafar gida za ta kai #45,000; Shinkafa yar waje za ta kai N80,000; lemun Coca-cola zai zama N300, kuma za a siyar da ruwan leda akan kudi biyu N100.

Kara karanta wannan

Hawaye sun kwaranya yayin da jami'in soja ya mutu a hanyarsa ta zuwa daurin aurensa

“Biskiti zai kai N100, N150, N200 yayin da kwalban mai zai kaii #2,000. Idan har gwamnati ba ta saurari shawarata ba a yanzu, tattalin arzikin zai yi kasa fiye da abin da muke fada.”

Rikici zai shiga tsakanin Tinubu da Wike, Ayodele

A baya mun ji cewaPrimate Elijah Ayodele, ya yi hasashen abubuwan da za su faru da wasu manyan mutane kamar su Shugaban kasa Bola Tinubu, ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike da shugaban IPOB a 2024.

A cewar Ayodele, Allah ya nuna masa wasu abubuwa, da ke nuna cewa za a samu sabanin siyasa da zai kai ga barkewar rikici tsakanin Shugaban kasa Bola Tinubu da Nyesom Wike.

Asali: Legit.ng

Online view pixel