Alison Madueke Ta Roki Tinubu Ya Bari Ta Dawo Najeriya, Ta Tona Asirin Gwamnan PDP? Gaskiya Ta Fito

Alison Madueke Ta Roki Tinubu Ya Bari Ta Dawo Najeriya, Ta Tona Asirin Gwamnan PDP? Gaskiya Ta Fito

  • Tsohuwar ministar man fetur ta Najeriya, Diezani Alison-Madueke ta musanta rahotannin da aka yaɗa kan wata hira da aka ce ta yi
  • Alison-Madueke, wacce ta tsere daga Najeriya a shekarar 2015, kuma tana fuskantar tuhume-tuhumen cin hanci da rashawa a Najeriya da Birtaniya, ta bayyana rahotannin a matsayin "ƙarya"
  • Tattaunawar da tsohuwar ministar ta musanta ta yi iƙirarin cewa ta na son amsa laifin almundahanar kuɗi tare da zargin gwamnan jihar Zamfara Dauda Lawal a badaƙalar cin hanci da rashawa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Landan, UK - Diezani Alison-Madueke, tsohuwar ministar man fetur ta musanta cewa an yi wata hira da ita a Landan kwanan nan inda ta roƙi Shugaba Bola Tinubu da ya bar ta ta dawo gida.

Kara karanta wannan

PDP ta nemi EFCC ta ba Gwamnan Zamfara hakuri kan wallafar da ta yi a soshiyal midiya

A ranar Asabar, 23 ga watan Disamba ne wasu kafafen sada zumunta suka yaɗa cewa tsohuwar ministar ta yi magana da ƴan jarida a Landan, inda ta zargi gwamnan jihar Zamfara mai ci, Dauda Lawal.

Diezani ta musanta yin hira da yan jarida
Alison Madueke ta musanta yin hira da yan jarida a Landan Hoto: WOLE EMMANUEL/AFP
Asali: Getty Images

An kuma yaɗa saƙon ne a shafin hukumar da ke yaƙi da masu yi wa tattalin arziƙin ƙasa zagon ƙasa (EFCC) ta Instagram amma daga baya aka goge shi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mai magana da yawun hukumar EFCC, Dele Oyewale ya ce ba a bada izinin yin wallafar ba.

Alison-Madueke ta musanta yin hirar

Da take mayar da martani a wata hira da jaridar Premium Times, Alison-Madueke ta ce ba ta yi wata hira ba kwanan nan, kuma ta bayyana rahoton a matsayin "ƙarya" da "ƙanzon kurege."

"Ban yi hira da kowa ba, domin haka ban faɗi ko ɗaya daga cikin abubuwan da aka danganta da ni ba. Labari ne na karya da aka tattara saboda dalilan da ban sani ba." A cewarta.

Kara karanta wannan

Ministan Tinubu ya dauki muhimmin alwashi kan kawo karshen ta'addanci a kasar nan

Me aka ce Alison-Madueke ta faɗa a hirar

A cikin hirar da aka yi da ita, Alison-Madueke ta roƙi Shugaba Tinubu da ya ba ta damar komawa Najeriya ta kuma amsa laifin tafka almundahana a lokacin da take minista.

Ta bayyana shirinta na bayyana bayanan kuɗaɗen da ake zargin ta karkatar da su.

PDP Ta Buƙaci EFCC Ta Nemi Afuwa

A wani labarin kuma, kun ji cewa jam'iyyar PDP reshen jihar Zamfara ta buƙaci hukumar EFCC ta nemi afuwa kan wani rubutu da ta yi a Instagram.

Jam'iyyar ta buƙaci hakan ne bayan hukumar ta yi wani rubutu wanda ya alaƙanta gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, da badaƙalar cin hanci da rashawa ta Diezani Alison Madueke.

Asali: Legit.ng

Online view pixel