An Samu Asarar Rayukan Mutum 11 Cikin Wani Yanayi Mara Dadi a Jihar Jigawa

An Samu Asarar Rayukan Mutum 11 Cikin Wani Yanayi Mara Dadi a Jihar Jigawa

  • Wani mummunan hatsarin mota ya ritsa da wasu motoci biyu a jihar Jigawa a ranar Asabar, 23 ga watan Disamba
  • Hatsarin motan wanda ya auku bayan motocin biyu sun yi taho mu gama da juna, ya yi sanadiyyar rasuwar mutum 11 nan take
  • Hatsarin dai ya auku ne a garin Kwanar Gujungu, ya ritsa ne da wata mota ƙirar Honda LE da wata mota ƙirar Golf

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Jigawa - Aƙalla mutum 11 ne aka tabbatar da rasuwarsu bayan wani mummunan hatsarin mota da ya auku a garin Kwanar Gujungu da ke jihar Jigawa.

Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ƴan sandan jihar, DSP Lawan Shiitu Adam, ya tabbatar da aukuwar lamarin a cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai a ranar Lahadi, cewar rahoton The Punch.

Kara karanta wannan

Rundunar yan sanda ta yi martani bayan dan sanda ya bindige jarumin fim, ta fadi matakin dauka

Hatsarin mota ya ritsa da mutum 11 a Jigawa
Mutum 11 sun rasu a wani hatsarin mota a Jigawa Hoto: FRSC Nigeria
Asali: UGC

Ya ce hatsarin ya auku ne a ranar Asabar inda wata mota ƙirar Honda LE da wata ƙaramar mota ƙirar Golf suka yi karo da juna, sakamakon haka dukkanin mutum 11 da ke cikin motocin biyu sun rasa rayukansu a nan take, rahoton Daily Post ya tabbatar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda hatsarin ya auku

Wani ɓangare na sanarwar na cewa:

"Hatsarin ya auku ne a ranar Asabar lokacin wata mota ƙirar Honda L.E launin toka mai lamba NSR 469 AE ɗauke da fasinjoji biyar daga Kano ta nufi garin Balangu ƙaramar hukumar Kafin Hausa da wata motar Golf mai lamba AUY 292 XA ɗauke da fasinjoji huɗu daga Gujungu zuwa ƙaramar hukumar Taura, suka yi karo wanda ya yi sanadin mutuwar mutum 11."
"Da samun rahoton, tawagar yan sanda daga sashin kula da zirga-zirgar ababen hawa, hedkwatar ƴan sanda ta Taura, sun garzaya wurin da lamarin ya faru, inda suka kai gawarwakin zuwa babban asibiti, inda wani likita ya tabbatar da rasuwarsu."

Kara karanta wannan

Ministan Tinubu ya dauki muhimmin alwashi kan kawo karshen ta'addanci a kasar nan

Rayuka Sun Salwanta a Wani Hatsarin Mota

A wani labarin kuma, kun ji cewa an samu asarar rayukan mutum biyu a wani mummunan hatsarin mota da ya auku a jihar Ogun.

Hukumar kiyaye haɗura ta ƙasa (FRSC) ta ce hatsarin ya ritsa da wasu motoci biyu ne a hanyar Idiroko zuwa Ota cikin dare.

Asali: Legit.ng

Online view pixel