“Sai Sun Fi Halin Bera”: Jigon APC Ya Hango Babbar Matsala Tattare da Yan Siyasa Masu Tasowa

“Sai Sun Fi Halin Bera”: Jigon APC Ya Hango Babbar Matsala Tattare da Yan Siyasa Masu Tasowa

  • Babban jigon APC kuma tsohon gwamnan Osun, Cif Bisi Akande ya yi hasashe kan yan siyasa masu tasowa a kasar
  • Akande ya bayyana cewa yan siyasa masu tasowa za su fi na yanzu tafka barna da suka hada da cin hanci da rashawa, mugunta da sauransu
  • Dattijon ya ce wadannan lalatattun yan siyasa za su yi gagayya da na yanzu bayan sun zarge su da rashawa, sannan a karshe su za su wawashe kasar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Tsohon gwamnan jihar Osun, Cif Bisi Akande ya ce babu lokacin da matsalar cin hanci da rashawa ta za zo karshe a Najeriya, illa ta ci gaba da wanzuwa, rahoton Vanguard.

Ya bayyana hakan ne a wajen bikin kaddamar da gidauniyarsa ta Adebisi Akande, wanda aka gudanar a garin Ibadan, babban birnin jihar Oyo.

Kara karanta wannan

Abin da yan bindiga suka fada mana kafin mu gano gawar Nabeeha, Kawunta

Bisi Akande ya magantu kan yan siyasa masu tasowa
“Sai Sun Fi Halin Bera”: Jigon APC Ya Hango Babbar Matsala Tattare da Yan Siyasa Masu Tasowa Hoto: MHR Clement Akanni
Asali: Twitter

A cewarsa, yan siyasar da za a samu a kasar a nan gaba, za su fi na yanzu cin hanci da aikata rashawa, bisa ga dukkan yadda alamu suka nuna.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yan siyasa masu tasowa za su fi aika-aika, Akande

Cif Akande ya kuma gargadi gwamnoni da sauran yan siyasa, musamman mambobin jam’iyyar APC mai mulki akan su yi hankali da lalatattun yan siyasa masu tasowa.

Ya ce wadannan ya siyasa za su zo su kalubalance su sannan su zarge su da aikata rashawa don su karbe madafun iko.

Akande, wanda ya kasance tsohon shugaban jam’iyyar APC na kasa, ya ce yana jin tsoro saboda yan Najeriya na magana kan rashawa a tsakanin shugabannin siyasar yanzu.

Inda ya ce wasu lalatattun yan siyasa na zuwa wadanda za su kasance masu cin hanci da rashawa, mugunta, arziki, da tasiri fiye da na yanzu.

Kara karanta wannan

Nasara a Kotun Koli: Abba Gida-Gida ya samu kyakkyawar tarba yayin da ya koma Kano ta hanyar Kaduna

Jigon na APC ya kara jaddada cewa yan siyasar masu tasowa za su yi takara ne don neman madafun iko tare da shugabannin yanzu kuma da alama su yi nasara amma a karshe su wawashe kasar, rahoton Punch.

Taron kaddamar da gidauniyar ya samu halartar manyan baki irin su Babajide Sanwo-Olu, gwamnan jihar Legas wanda ya wakilci shugaban kasa Bola Tinubu.

Haka kuma gwamnan Borno Babagana Zulum ya halarci taron, inda shi kuma ya wakilci mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima; da sauransu.

An yi bikin cikar Akande shekaru 85

A baya mun ji cewa manyan jiga-jigan Najeriya sun fara isa cibiyar taro na kasa da kasa da ke jami'ar Ibadan, domin taya tsohon shugaban jam'iyyar APC na kasa, Cif Bisi Akande, murnar cika shekaru 85 a duniya.

Yayin taron an kuma tsara za a kaddamar da wata gidauniya ta Adebisi Akande, rahoton The Nation.

Asali: Legit.ng

Online view pixel