Gwamnan PDP Ya Cire Tsoro Ya Bayyana Masu Taimakawa Yan Bindiga a Jiharsa

Gwamnan PDP Ya Cire Tsoro Ya Bayyana Masu Taimakawa Yan Bindiga a Jiharsa

  • Gwamnan jihar Plateau, Caleb Mutfwang ya yi zargin cewa akwai hannun wasu jami'an tsaro a matsalar rashin tsaron da ake fama da ita
  • Gwamnan ya yi nuni da cewa ɓata-gari sun yi kutse cikin jami'an tsaro inda suka zama wakilan masu aikata laifuka
  • Gwamna Mutfwang ya shawarci gwamnatin tarayya da ta tabbatar cewa an sanya lura a ɗaukar jami'an tsaron da ake yi yanzu

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Plateau - Gwamnan jihar Plateau, Celeb Mutfwang, ya nuna damuwarsa game da kutsen da miyagu suka yi a cikin jami’an tsaro.

Gwamnan ya yi zargin cewa wasu jami’an tsaro suna aiki a matsayin wakilan masu aikata laifuka.

Gwamnan Plateau ya zargi wasu jami'an tsaro
Gwamna Caleb ya yi zargin cewa akwai hannun wasu jami'an tsaro a matsalar rashin tsaro Hoto: Caleb Mutfwang
Asali: Facebook

Da yake magana a gidan talabijin na Trust TV jiya Laraba, Mutfwang ya koka kan batutuwa da dama da suka shafi tsaro da hulɗar jama'a, inda ya bayyana wasu lokutan da jami'an tsaro suka ƙwace makamai gama gari kamar adduna daga hannun mutane.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai kazamin hari ofishin jami'an tsaro, sun tafka mummunar ɓarna da kisa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mutfwang ya yi kira da a yi nazari mai muhimmanci kan tsarin ɗaukar jami'an tsaro da kuma hanyar da za a kawar da "ɓata-gari" a cikin ayyukan tsaro.

Ya kuma jaddada buƙatar a ƙara ƙaimi wajen tabbatar da gaskiya kula da mallakar makamai.

Wane zargi Gwamna Mutfwang ya yi?

A kalamansa:

"Bari na faɗa cewa an kutsa cikin jami’an tsaro, wannan ita ce gaskiyar da ya kamata mu fuskanta a matsayinmu na ƙasa. Akwai mutane da yawa a cikin jami’an tsaro waɗanda bai kamata su kasance a wurin ba.
"Sun kasance wakilan waɗannan miyagun ne, wani lokacin ma su kan sayar da rayukan abokan aikinsu, shi ya sa ake yawan yin kwanton ɓauna a lokacin da waɗannan jami’an tsaro ke gudanar da ayyukansu.
"Don haka dole ne shugaban ƙasa ya bayar da kwakkwaran umarni ga jami’an tsaro cewa a ɗaukar jami'an tsaron da ake yi yanzu, dole ne a yi taka-tsan-tsan, a kuma lura da cewa ba a ɗauki wasu ɓata-gari da ba su dace ba a cikin jami’an tsaro."

Kara karanta wannan

Gwamna Makinde ya bayyana abin da ya haddasa tashin abin fashewa a Ibadan, bidiyo ya bayyana

An Cafke Masu Hannu a Hare-Haren Plateau

A wani labarin kuma, kun ji cewa rundunar ƴan sandan Najeriya ta tabbatar da cafke ƙarin mutum uku da ake zargin akwai hannunsu a hare-haren da aka kai a jihar Plateau.

Cafke miyagun dai na zuwa ne bayan an kama wasu mutum takwas da ake zargin akwai hannunsu a hare-haren na jajibirin ranar Kirsimeti a wasu ƙauyukan jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel