Tinubu Ya Bayyana Dalili 1 Da Ya Sa Buhari Ba Zai Iya Tserewa Zuwa Jamhuriyar Nijar Ba

Tinubu Ya Bayyana Dalili 1 Da Ya Sa Buhari Ba Zai Iya Tserewa Zuwa Jamhuriyar Nijar Ba

  • Shugaba Tinubu ya ce tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ba zai iya guduwa zuwa jamhuriyar Nijar kamar yadda ya yi alkawari zai yi ba saboda shi (Tinubu) ya rufe iyakokin Najeriya
  • Tinubu ya bayyana haka ne a wajen bikin baje kolin litattafai kan gwamnatin Buhari a babban birnin tarayya Abuja
  • Shugaba Tinubu ya ce ya yi matuƙar farin ciki da tarbar magabacinsa a Abuja, yana mai bayyana shi a matsayin babban mutum, kuma mai kishin ƙasa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Shugaba Bola Tinubu ya ce magabacinsa, Muhammadu Buhari, ba zai iya komawa Jamhuriyar Nijar ba kamar yadda ya yi alƙawari saboda rufe iyakokin ƙasar nan.

Buhari ya ce zai tafi makwabciyar ƙasar nan Jamhuriyar Nijar bayan ya miƙa masa shugabancin ƙasar nan, idan bai samu isasshen hutu ba a garin Daura, mahaifarsa a jihar Katsina.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya fadi hanya 1 da zai bi wajen magance matsalar rashin tsaro a Najeriya

Tinubu ya yi magana kan komawar Buhari Nijar
Shugaba Tinubu ya ce Buhari ba zai iya komawa Nijar ba Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Tinubu ya yi matukar farin ciki da haɗuwa da Buhari

Sai dai da yake magana, a lokacin ƙaddamar da littattafan, Tinubu cikin raha ya ce magabacinsa ba zai iya cimma hakan ba saboda rufe iyakokin ƙasar nan, cewar rahoton Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jaridar PM News ta ambato shugaban ƙasan ya bayyana cewa:

"Lokacin da Shugaba Buhari zai bar ofis ya ce zai yi ritaya zuwa Daura, mai nisa da Abuja don jin daɗi yadda ya kamata bayan ya yi ritaya daga aikin gwamnati.
"Na tuna ya ƙara da cewa idan magoya bayansa da abokansa suka hana shi samun isasshen hutu a Daura, zai gudu zuwa Jamhuriyar Nijar. To, kamar yadda kuka sani, ba zai iya tserewa zuwa Jamhuriyar Nijar ba, saboda rufe iyakokin ƙasar nan.
"Saboda haka na yi matuƙar farin cikin tarbarsa a nan Abuja."

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya fusata kan matsalar rashin tsaro, ya sha sabon alwashi

Tinubu Ya Gana da Hafsoshin Tsaro

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinuɓu ya gana da manyan hafsoshin tsaro na ƙasar a fadarsa dake birnin tarayya Abuja.

Shugaban ƙasar ya gana da manyan hafsoshin tsaron ne yayin da matsalar rashin tsaro take ƙara taɓarɓarewa a ƙasar nan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel