Manyan Labarai A Yau
Masu garkuwa da mutane sun sace wasu mutane da ba a san adadinsu ba a hanyar titin Akure/Ikere. Jami'ar Yan sanda Funmi Odunlami ta tabbatar da lamarin.
Karamin ministan tsaro Bello Matawalle ya shawarci yan Najeriya da su yi riko da al'adun juna domin kara bunkasa zaman lafiya da hadin kai a kasa.
An shiga jimami a jihar Benue bayan wata mummunar gobara ta lakume gidaje 50. Gobarar wacce ta tashi da safe ta janyo wata tsohuwa ta rasa ranta.
Dakarun sojin sama na Najeriya sun samu nasarar halaka wani kasurgumin shugaban yan ta'adda wanda ya dade yana addabar bayin Allah a jihar Kaduna.
Arzikin shugaban kamfanin BUA, Abdulsamad Rabiu, ya karu sosai wanda hakan ya sanya ya samu sabon matsayi a cikin jerin attajiran Najeriya da nahiyar Afirika.
Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC ta daukaka kan hukuncin da wata babbar kotu ta yanke na wanke tsohon gwamnan jihar Neja, Babangida Aliyu.
Babatunde Fashola ya ce ₦577,000 kawai yake karba kudin fansho a matsayinsa na tsohon gwamnan jihar Legas. Ya bayyana hakan ne a wata hira da aka yi da shi.
Rundunar yan sandan babban birnin tarayya Abuja, sun bayyana rahoton garkuwa da mutane a rukunin gidaje na River Park, Abuja a matsayin kanzon kurege.
Salihu Lukman ya bayyana cewa yana daga cikin wadanda suka yi gwagwarmayar fitar da tsohon shugaban APC, Abdullahi Adamu da sakatariyar jam’iyyar, Iyiola Omisore.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari