Badakalar N4bn: EFCC Ta Maka Tsohon Gwamna da Tsohon Shugaban PDP a Gaban Kotu

Badakalar N4bn: EFCC Ta Maka Tsohon Gwamna da Tsohon Shugaban PDP a Gaban Kotu

  • Hukumar EFCC ta ɗaukaka ƙara kan hukuncin da wata babbar kotun jihar Neja da ke Minna ta yanke kan tsohon gwamnan jihar, Babangida Aliyu bisa zargin almundahanar 4bn
  • Wani wanda ake tuhuma a cikin laifin zambar ɗin N4bn shi ne tsohon shugaban jam'iyyar PDP a jihar Neja, Tanko Beji
  • Sauran waɗanda ake tuhuma da laifin zambar sun haɗa da tsohon kwamishinan muhalli kuma shugaban ma’aikata na Babangida Aliyu, Umar Nasko

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Minna, jihar Neja - Hukumar yaƙi da yi wa tattalin arziƙin ƙasa ta’annati (EFCC) ta garzaya kotu domin ɗaukaka ƙara kan hukuncin da aka yanke wa Babangida Aliyu, tsohon gwamnan jihar Neja da Tanko Beji, tsohon shugaban jam’iyyar PDP a jihar.

Kara karanta wannan

Bayan nasara a Kotun Koli, gwamnan APC ya aike da sako mai zafi ga dan takarar PDP

Hukumar EFCC ta bayyana hakan a wani sako da ta wallafa a shafinta na twitter a ranar Alhamis, 8 ga watan Janairu, inda ta ƙara da cewa ana tuhumar su da laifuffuka bakwai da suka haɗa da haɗa baki, cin zarafi da kuma cin amana.

EFCC ta maka Babangida Aliyu kotu
EFCC ta maka tsohon gwamnan Neja gaban kotu kan badakalar N4bn Hoto: EFCC Nigeria
Asali: Twitter

Yadda kotun Neja ta saki tsohon gwamna Aliyu kan almundahanar N4bn

Ku tuna cewa mai shari'a Abdullahi Mika'ilu na babbar kotun jihar Neja, ya wanke tsohon gwamnan da tsohon shugaban jam'iyyar PDP kan zargin almundahanar N4bn a ranar 7 ga watan Disamban 2023.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A tuhume-tuhume bakwai da suka shafi zamba da cin amana da EFCC ta shigar a gaban mai shari’a Mayaki, mai ritaya, tsohon gwamna Aliyu, Beji, tsohon kwamishinan muhalli kuma shugaban ma’aikata na Babangida Aliyu, Umar Nasko, su ne waɗanɗa ake ƙara.

Kara karanta wannan

Gwamnan APC, tsoffin gwamnoni 2 da wasu manyan ƙusoshi sun dira Kotun Koli ana shirin yanke hukunci

EFCC ta daukaka ƙara kan zargin zambar N4bn da ake yi wa Aliyu

Sai dai wadanda ake tuhumar sun buƙaci yin watsi da ƙarar a gaban alƙali. Daga bisani ya amsa buƙatarsu a watan Disamba.

Sai dai hukumar EFCC ta nuna rashin gamsuwarta da hukuncin da kotun yanke na ƴanta Aliyu da Beji don haka ta shigar da ƙara a ranar 10 ga watan Janairun 2024.

FG Ta Shigar da Sabbin Tuhume-Tuhume Kan Emefiele

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin tarayya ta sake shigar da sababbin tuhume-tuhume kan tsohon gwamnan CBN, Godwin Emefiele.

Sababbin tuhume-tuhumen sun haɗa da amfani da takardun jaɓu, bayar da cin hanci da rashawa, da kuma cin amana da sauransu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel