Ana Cikin Matsalar Rashin Tsaro, Ministan Tsaro Ya Fadi Abu 1 da Ya Kamata Yan Najeriya Su Yi

Ana Cikin Matsalar Rashin Tsaro, Ministan Tsaro Ya Fadi Abu 1 da Ya Kamata Yan Najeriya Su Yi

  • Ƙaramin ministan tsaro Bello Matawalle ya shawarci ƴan Najeriya da su yi riƙo da juna ta hanyar mutunta al'adun da ake da su a ƙasar nan
  • Ministan ya yi nuni da cewa hakan ne zai ƙara tabbatar da haɗin kai a tsakanin al'ummar ƙasar nan mai al'adu da harsuna daban-daban
  • Matawalle ya kuma bayar da tabbacin jajircewar shugaban ƙasa Bola Tinubu wajen ganin tsaro ya inganta ƙasa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Ƙaramin ministan tsaro, Dakta Bello Matawalle, ya yi kira ga ƴan Najeriya da su rungumi al’adu daban-daban da suka haɗa su a matsayin ƙasa.

Matawalle ya yi wannan roƙon ne a matsayin babban bako na musamman a wajen bikin rundunar sojin saman Najeriya na (BASA 2023) da aka gudanar a sansanin rundunar da ke Abuja, cewar rahoton PM News.

Kara karanta wannan

Dakarun sojoji sun sheke manyan kwamandojin yan ta'adda, sun ceto mutum 27

Matawalle ya shawarci yan Najeriya
Matawalle ya shawarci yan Najeriya su mutunta al'adun juna Hoto: Bello Matawalle
Asali: Twitter

A cewarsa, al'adunmu da harsuna suna da banbance-banbance kamar yadda suke da kyau, suna tattare da fahimtar al'umma da tsayin daka wanda ya haɗa mu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya lura cewa ta hanyar bukukuwa irinsu BASA ne ƴan Najeriya za su iya godiya da irin gudunmawar da kowace al'ada ta bayar don bunƙasa fahimta da haɗin kai.

Matawalle ya yabi rundunar sojin sama

Ya kuma yabawa rundunar sojin saman Najeriya bisa karramawa da kuma ba da kyaututtuka ga sojoji maza da mata waɗanda suka yi fice a wajen aikinsu.

Ministan ya kuma tabbatar wa da ƴan Najeriya ajandar sabunta fata ta Shugaba Bola Tinubu domin tabbatar da tsaron ƙasa.

A kalamansa:

"Shugaban ƙasa tun bayan hawansa mulki ya ba da fifiko kan buƙatun tsaro na rundunar soji.
"Wannan ya bayyana a cikin kuɗaɗe da kuma zuba jari a cikin kayan aiki na zamani don inganta ƙarfin sojojin, don tabbatar da cewa sun ci gaba da kasancewa runduna mafi girma da ake ji da ita.

Kara karanta wannan

Hukuncin Kotun Koli: Dan takarar PDP ya aike da sako mai muhimmanci bayan rigima ta barke a Arewa

Matawalle Ya Amince Ya Yi Aiki Tare da Gwamna Dauda

A wani labarin kuma, kun ji cewa ƙaramin ministan tsaro, Bello Matawalle ya amince ya yi aiki tare da Gwamna Dauda Lawal na Zamfara.

Matawalle ya ce sun karbi hukuncin Kotun Koli hannu bibbiyu kuma su na yi wa Gwamna Dare fatan alkairi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng