Sarkin Tikau, Alhaji Muhammadu Abubakar Ya Riga Mu Gidan Gaskiya

Sarkin Tikau, Alhaji Muhammadu Abubakar Ya Riga Mu Gidan Gaskiya

  • Allah ya yi wa mai martaba Sarkin Tiƙau a jihar Yobe, Alhaji Muhammadu Abubakar Ibn Grema rasuwa ranar Jumu'a da yamma
  • Basaraken ya rasu bayan fama da rashin lafiya ta tsawon lokaci a asibitin kwararru da ke garin Potiskum a jihar Yobe
  • Marafa na Tiƙau, Alhaji Shaibu Baba Alaraba, ya bayyana marigayi sarkin a matsayin mutum mai tausayi da sadaukar da kai domin al'ummarsa

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Yobe - Sarkin Tikau na jihar Yobe, Alhaji Muhammadu Abubakar Ibn Grema ya riga mu gidan gaskiya.

Iyalan marigayin ne suka tabbatar da rasuwar Sarkin da yammacin ranar Jumu'a, 10 ga watan Mayu, 2024, kamar yadda jaridar Leadership ta ruwaito.

Kara karanta wannan

InnalilLahi: 'Yan bindiga sun bindige ma'aikacin FIRS a tsakiyar birnin Abuja

Sarkin Tikau, Muhammadu Abubakar Ibn Grema.
Allah ya yi wa mai martaba Sarkin Tikau, Alhaji Muhammadu Abubakar rasuwa Hoto: Aubakar Siddiqui Ibn Muhammad
Asali: Facebook

Sarkin ya rasu ne a Asibitin kwararru da ke garin Potiskum bayan ya sha fama da rashin lafiya ta tsawon lokaci wanda ya hana shi shiga harkokin jama'a.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Marigayi Sarkin, wanda ya rasu yana da shekaru 74 a duniya, ya bar mata uku, ƴaƴa da jikoki da dama.

Kanin sarkin, Alhaji Abubakar Talba, ya tabbatar da rasuwar a wata hira da kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) a Damaturu ranar Asabar.

Talba, yarima a masarautar Tikau, ya ce Ibn-Grema ya rasu a Potiskum da misalin karfe 4 na yammacin ranar Juma’a, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

“Eh haka ne, Allah ya yi wa Sarki rasuwa bayan fama da rashin lafiya. Ya haura shekaru 70 a duniya,” in ji shi.

Yariman ya ce za yi wa marigayin jana’iza da misalin karfe 4 na yamma ranar Asabar kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.

Kara karanta wannan

Bayan Rahama Sadau, wata jarumar fina finai ta sake samun mukami a Abuja

Marafa na Tiƙau ya yi ta'aziyya

A halin da ake ciki, Marafa na Tikau, Alhaji Shaibu Baba Alaraba, ya aike da saƙon ta'aziyya bisa rasuwar sarkin.

Ya bayyana marigayin a matsayin shugaba na gari kuma mutum ne mai kima a cikin al’umma, wanda aka san shi da hikima, tausayi da sadaukar da kai domin inganta rayuwar al’ummarsa.

Ya kuma fahimci irin gudunmawar da marigayi Sarkin ya bayar wajen ci gaban Yobe da kuma irin tasirin da yake da shi ga al’umma.

An kashe babban malami a Zamfara

A wani rahoton kuma Yan bindiga sun kai hari kauyukan manoma a kananan hukumomin Maradun da Tsafe a jihar Zamfara ranar Alhamis da ta wuce.

Rahoto daga yankin ya nuna cewa daga cikin waɗanda aka kashe har da wani babban malamin Musulunci, Mallam Makwashi Maradun.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel