Jam'iyyar PDP Ta Gayawa Tinubu Gaskiyar Halin da Ake Ciki a Kasa, Ta Ba Shi Shawara

Jam'iyyar PDP Ta Gayawa Tinubu Gaskiyar Halin da Ake Ciki a Kasa, Ta Ba Shi Shawara

  • Jam'iyyar adawa ta PDP ta nuna takaicinta kan halin yunwa, talauci da tsadar rayuwa da ƴan Najeriya suke fama da shi
  • Jam'iyyar ta ɗora alhakin komai a kan shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu da jam'iyyarsa ta APC mai mulki a Najeriya
  • PDP ta shawarci shugaban ƙasan da ya saurari kiraye-kirayen da ƴan Najeriya ke yi na ya sauya wasu tsare-tsarensa da suka jefa mutane cikin wahala

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishɗi

FCT, Abuja - Jam’iyyar PDP ta zargi jam’iyyar APC da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu da jefa ƴan Najeriya cikin tsabagen wahala da talauci.

Jam'iyyar adawan ta bayyana cewa ƴan Najeriya sun fusata kan halin da ƙasar nan ke ciki.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar APC ta fusata kan kalaman Atiku da PDP ga Tinubu, ta yi martani mai zafi

Jam'iyyar PDP ta caccaki Tinubu
Jam'iyyar PDP ta caccaki gwamnatin Tinubu Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

PDP ta caccaki jam'iyyar APC

Jam’iyyar PDP ta kuma ce jam’iyyar APC ta tozarta tsarin dimokuradiyya wanda marigayi Cif MKO Abiola ya yi fafutuka a kai, cewar rahoton jaridar Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jam’iyyar PDP ta bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labaranta na ƙasa, Debo Ologunagba, ya fitar, rahoton The Punch ya tabbatar.

PDP ta bukaci ƴan Najeriya da su yi amfani da bikin ranar dimokuradiyya na bana wajen nuna adawa da tsare-tsaren APC waɗanda suka jefa mutane cikin wahala.

"Abin takaici ne ƙasarmu na bikin ranar dimokuraɗiyya a ƙarƙashin gwamnatin da ta yi fice wajen maguɗin zaɓe, keta kundin tsarin mulki, tauye ƴan adawa domin mayar da Najeriya ƙarƙashin jam'iyya ɗaya."
"Abu mafi takaici shi ne dukkanin ci gaban da gwamnatocin PDP suka samu wajen bunƙasa dimokuraɗiyya a Najeriya, gwamnatocin APC sun share su."

Kara karanta wannan

Atiku ya fadi babban mai laifi kan halin kuncin da ake ciki a Najeriya

- Debo Olugunagba

Wace shawara PDP ta ba Tinubu?

Jam'iyyar PDP ta buƙaci shugaban ƙasan da ya yi amfani da wannan lokacin wajen yin tunani kan halin da ƙasar nan ke ciki a a ƙarƙashin mulkinsa duba da yadda ake ta ƙorafi kan yunwa da tsadar rayuwa a ƙasar.

PDP ta tunatar da shugaban ƙasan cewa akwai talauci a ƙasa kuma ya kamata ya saurari ƴan Najeriya domin sake tsare-tsarensa waɗanda suka jefa mutane cikin wahala.

Atiku ya caccaki jam'iyyar APC

A wani labarin kuma, kun ji cewa ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP a zaɓen 2023, Atiku Abubakar, ya ɗora alhakin halin ƙuncin da ƴan Najeriya suke ciki kan jam’iyyar APC.

Tsohon mataimakim shugaban ƙasan ya kuma soki jam'iyyun adawa kan yadda suka haɗewa waje ɗaya domin kawo ƙarshen mulkin APC a ƙasar nan.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng