Dakarun Sojoji Sun Hallaka Rikakken Shugaban 'Yan Bindiga da Mayakansa 35 a Arewa

Dakarun Sojoji Sun Hallaka Rikakken Shugaban 'Yan Bindiga da Mayakansa 35 a Arewa

  • Dakarun sojojin Najeriya sun samu nasara a ƙoƙarin da suke yi na kawo ƙarshen ƴan bindigan da suka addabi mutane a ƙasar nan
  • Sojojin sun samu nasarar hallaka wani gawurtaccen shugaban ƴan bindiga, Buharin Yadi a yayin wani artabu a ƙaramar hukumar Giwa ta jihar Kaduna
  • Jami'an tsaron sun kuma hallaka mayaƙansa mutum 35 a artabun da suka yi a cikin daji da miyagun ƴan bindigan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kaduna - Dakarun sojoji na rundunar Operation Whirl Punch, sun hallaka riƙaƙƙen shugaban ƴan bindiga, Buhari Alhaji Halidu, wanda aka fi sani da Buharin Yadi a jihar Kaduna.

Sojojin sun hallaka gawurtaccen ɗan bindigan ne yayin wani artabu a ƙaramar hukumar Giwa ta jihar.

Kara karanta wannan

Gwamna ya yi martani yayin da sojoji suka hallaka shugaban 'yan bindiga

Sojoji sun hallaka shugaban 'yan bindiga a Kaduna
Dakarun sojoji sun hallaka shugaban 'yan bindiga, Buharin Yadi a Kaduna Hoto: @HQNigerianArmy
Asali: Facebook

Sojoji sun hallaka shugaban ƴan bindiga

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar, Samuel Aruwan, ya fitar, cewara rahoton tashar Channels tv.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kwamishinan ya bayyana cewa Buharin Yadi tare da mayaƙansa mutum 35 sun gamu da ajalinsu ne bayan sun fafata da dakarun sojojin.

Dakarun sojojin ƙarƙashin jagorancin kwamandan rundunar, Manjo Janar Mayirenso Saraso, sun je aiki ne a dajin Idasu da ke iyaka da ƙaramar hukumar Giwa a Kaduna da ƙaramar hukumar Sabuwa a jihar Katsina.

Yadda sojoji suka hallaka Buharin Yadi

Dakarun sojojin sun fara aikin ne bayan sun samu bayanan sirri kan motsin ƴan ta'adda daga Saminaka da Saulawa na jihar Katsina, rahoton jaridar Tribune ya tabbatar.

Bayan sun isa Saminaka, sojojin sun tarar da an lalata wani ƙauye tare da kashe shanu, wanda hakan ya nuna ƴan bindiga sun ziyarci wajen.

Kara karanta wannan

Dakarun sojoji sun hallaka 'yan ta'adda yayin artabu a jihar Kaduna

Dakarun sojojin sun yi musayar wuta da ƴan bindigan ne a Hayin Almajiri bayan sun yi musu kwanton ɓauna. Binciken da aka yi ya nuna cewa an hallaka aƙalla ƴan bindiga mutum 36.

Daga baya an tabbatar da cewa daga cikin waɗanda suka sheƙa barzahu akwai Kachalla Buharin Yadi.

Sojoji sun samu yabo

Legit Hausa ta tuntuɓi wani mazaunin ƙaramar hukumar Giwaai suna Abdulmalik Sani wanda ya nuna jin daɗinsa kan wannan nasara da sojojin suka samu.

Abdulmalik ya bayyana cewa nasarar abin a yaba kuma dama sun daɗe suna addu'ar Allah ya kawo musu sauƙi kan matsalar rashin tsaron da ake fama da ita a yankin.

A kalamansa:

"Eh tabbas wannan babbar nasara ce kuma muna dama fatanmu kenan jami'an tsaro su riƙa samun nasara kan miyagun da suka addabi mutane."

Sojoji sun hallaka ƴan bindiga

A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojoji na Operation Whirl Punch sun kashe ƴan bindiga biyar a yankin Dantarau na ƙaramar hukumar Kajuru a jihar Kaduna.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun tare hanyar Kaduna zuwa Abuja, sun sace fasinjoji masu yawa

Dakarun sojojin sun je wani aikin sintiri ne a yankin Kachia-Kajuru a lokacin da suka ci karo da ƴan bindigan da suka addabi mutanen yankin.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng