Manyan Labarai A Yau
Gwamnan Rivers, Siminalayi Fubara, ya yi martani kan wa'adin kwanaki bakwai da 'yan majalisar dokokin jihar suka ba shi. Gwamnan ya ce su ba 'yan majalisa ba ne.
Gwamnatin jihar Borno ta samar da tsarin mayar da tubabbun 'yan ta'addan Boko Haram zuwa cikin al'umma. Ya zuwa yanzu ta mayar da mutum 8,940 da suka tuba.
Jami'an hukumar kwastam a kasar Sin sun kama wani matashi dauke da macizai 104 yana kokarin safararsu ta barauniyar hanya. Sun bayyana abin da za a masa.
Wasu fusatattun mazauna masarautar Rano a jihar Kano sun kori wakilin da Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, ya tura zuwa masarautar da aka rushe.
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya rantsar da manyan sakatarori takwas na tarayya. Shugaban kasan ya ba su rantsuwar kama aiki ne a fadarsa da ke Abuja.
Kotun Koli ta shirya yanke hukunci a karar da gwamnatin tarayya ta shiyar da gwamnoni 36 na kasar nan kan neman cikakken 'yancin cin gashin kan kananan hukumomi.
Jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta garzaya kotun daukaka kara kan hukuncin babbar kotun tarayya na soke zaben fidda gwaninta na gwamnan jihar Edo.
Zargin karkatar da N1.5bn ya sanya majalisar wakilai ta gayyato ministar harkokin mata Uju Kennedy Ohuneye. Kwamitin majalisar ya yi mata tambayoyi.
Wasu miyagun 'yan bindiga sun hallaka mutum biyu a wani hari da suka kai a karama hukumar Kachia ta jihar Kaduna. 'Yan bindigan sun kuma sace wasu mutane.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari