Kotun Koli Ta Shirya Yanke Hukunci Kan Karar da Gwamnatin Tarayya Ta Shigar da Gwamnoni

Kotun Koli Ta Shirya Yanke Hukunci Kan Karar da Gwamnatin Tarayya Ta Shigar da Gwamnoni

  • Kotun Ƙoli ta bayyana cewa za ta yanke hukunci kan ƙarar da gwamnatin tarayya ta shigar da gwamnoni 36 kan neman cikakken cin ƴancin gashin kai ga ƙananan hukomomi
  • Kotun za ta yanke hukunci a ranar Alhamis, 11 ga watan Yuli kan ƙarar wacce gwamnatin tarayya ƙarƙashin jagorancin Shugaba Bola Tinubu ta shigar da gwamnonin
  • Tuni Kotun Ƙolin ta sanar da ɓangarorin da ke cikin ƙarar kan ranar yanke hukuncin ta hannun lauyoyinsu da ke wakiltarsu a ƙarar

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Kotun ƙoli ta shirya yanke hukunci kan ƙarar da gwamnatin tarayya ta shigar da gwamonin 36 na ƙasar nan.

Gwamnatin tarayya ta shigar da ƙarar ne domin neman cikakken ƴancin cin gashin kai ga ƙananan hukumomi 774 na ƙasar nan.

Kara karanta wannan

PDP ta dauki mataki bayan kotu ta soke zaben fidda gwaninta na gwamna

Kotun Koli za ta yanke hukunci
Kotun Koli za ta yanke a shari'ar gwamnatin tarayya da gwamnoni Hoto: @OfficialABAT
Asali: Twitter

Yaushe Kotun Ƙoli za ta yanke hukuncin?

Jaridar The Nation ta ce Kotun Ƙolin za ta yanke hukunci kan ƙarar a gobe Alhamis, 11 ga watan Yulin 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wata takarda da aka gani ranar Laraba a Kotun Ƙoli ta nuna cewa an sanar da ɓnagarorin da ke cikn ƙarar ta hannun lauyoyinsu.

An ba gwamnatin tarayya sanarwar yanke hukuncin ta hannun ofishin Antoni Janar na tarayya kuma ministan shari'a a ma'aikatar shari'a da ke Abuja.

A ranar Alhamis, 13 ga watan Yuni, Kotun Ƙoli ta tanadi hukunci a ƙarar wacce gwamnatin tarayya take yi da gwamnoni 36 na ƙasar nan.

A wancan lokacin, mai Shari'a, Mohammed Lawal Garba wanda ya jagoranci alƙalan kotun guda bakwai ya ce za su bayyana ranar yanke hukuncin ƙarshe ga duka ɓangarorin

Mai shari'a Lawal Garba ya bayyana haka ne jim kaɗan bayan lauyoyin duka bangarorin sun gabatar da korafe-korafensu kan shari'ar.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta dauki matakin magance yunwar da ake yi a kasa

Gwamnatin Tinubu za ta raba taki

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin tarayya ƙarƙashin jagorancin Shugaba Bola Tinubu ta aika da tireloli 60 na takin zamani ga kowace jiha.

Gwamnatin ta kuma kowane sanata tirela biyu na takin domin rabawa a mazaɓarsa yayin sa aka ba ƴan majalisar wakilai tirela ɗaya su raba a mazaɓunsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng