Manyan Labarai A Yau
Tsohon sanatan Kaduna ta Tsakiya, Sanata Shehu Sani, ya bayyana cewa Allah ne kadai zai iya magance rikicin siyasar da ke tsakanin Gwamna Siminalayi Fubara da Wike.
An samu cece-ku-ce kan yarjejeniyar Samoa da gwamnatin Najeriya ta sanyawa hannu a makon da ya wuce. Legit ta fayyace gaskiya kan abin da yarjejeniyar ta kunsa.
Jam'iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) reshen jihar Kano ta yi watsi da korar da wani tsagin jam'iyyar ya yiwa Rabiu Musa Kwankwaso daga jam'iyyar.
'Yan ta'adda dauke da bindigu sun yi shigar mata inda suka sace mutane masu yawa a jihar Katsina. 'Yan ta'addan sanye da hijabai sun kai harin ne a Safana.
'Yan majalisar dokokin jihar Rivers, karkashin jagorancin Martins Ameuwhule sun ba Gwamna Siminalayi Fubara wa'adin kwana bakwai kan kasafin kudin 2024.
Kungiyar malaman jami'o'i ta Najeriya (ASUU) ta bayyana cewa za ta hakura ne kawai da shiga yajin aiki idan gwamnatin tarayya ta aiwatar da yarjejeniyar da suka yi.
Basaraken daular Yarabawa ta Ile-Ife, Ooni na Ife, Adeyeye Enitan Ogunwusi, ya samu sabuwar motar zinare. 'Yan Najeriya sun taya shi murna a shafukan sada zumunta.
Wasu miyagun 'yan bindiga su kai harin kwanton bauna kan jami'an tsaro na 'yan banga a jihar Imo. 'Yan bindigan sun hallaka mutum hudu ciko har da wani yaro.
Gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda, ya ba da hutu a jihar domin murnar shigowar sabuwar shekarar musulunci ta 1446AH. Gwamnan ya ce ba aiki a ranar Litinin.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari