Manyan Labarai A Yau
Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya koka kan kalubalen da yake fuskanta a fagen siyasar Najeriya. Ya ce ana tsangwamarsa da zaginsa.
Gwamnan jihar Kwara, Abdulrahman Abdulrazaq, ya ja kunnen 'yan ta'addan da suka addabi jihar. Ya gargade su kan su gudu tun kafin lokaci ya kure musu.
Tsohon dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar LP a zaben 2023, Peter Obi, ya shirya komawa jam'iyyar. Peter Obi ya sa lokacin da zai koma jam'iyyar ADC.
Wasu bama-bamai da ake zargin 'yan bindiga sun yi sanadiyyar hallaka mutane a jihar Zamfara. Bama-baman sun tashi ne lokacin da matafiya ke tafiya a motoci.
Dan majalisa a Amurka, Riley Moore, ya yi tsokaci kan harin da kasarsa ta kawo a Najeriya. Ya bayyana cewa harin ya hana kisan Kiristoci lokacin Kirsimeti
'Yan bindiga sun kulla yarjejeniya kan sulhu da mahukunta a karamar hukumar Malumfashi ta jihar Katsina. Sun sako mutanen da suka yi garkuwa da su.
Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Barau Jibrin, ya tarbi wasu jiga-jigan jam'iyyar NNPP da suka sauya sheka zuwa APC. Daga ciki har da hadimin Gwamna Abba.
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa gwamnatin tarayya na kokari wajen kawo karshen matsalar rashin tsaro. Ya ce ya nemi dauki kan matsalar.
Tsohon gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal ya yi martani kan harin da Amurka ta kawo Najeriya. Ya bukaci jama'a su kwantar da hankulansu.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari