Manyan Labarai A Yau
Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Ezenwo Wike, ya fito ya yi karin haske kan batun cewa sun samu sabani tsakaninsa da shugaban kasa Bola Tinubu.
Gwamna Monday Okpebholo na Edo ya kori Samson Osagie daga matsayin kwamishinan shari’a, ya kuma ƙara ma’aikatu zuwa 28 don daidaita tsarin gwamnati.
Babbar kotun tarayya a Abuja ta ƙi karbar bukatar DSS ta sake gabatar da hujjoji da aka ƙi karɓa a shari’ar tsohon NSA Sambo Dasuki, saboda wasu dalilan shari'a.
Bayan sauya sheka zuwa APC, Gwamna Peter Mbah ya ce ya kamata a warware matsalar Nnamdi Kanu ta sigar siyasa. Ya ce ya tattauna da Shugaba Tinubu kan hakan.
Jam'iyyar APC ta kara yawan sanatocin da take da su a majalisar dattawa. Sanata Samaila Dahuwa Kaila ya koma jam'iyyar APC bayan ya yi murabus daga PDP.
An yi babban rashi a jihar bayan rasuwar daya daga cikin shugabannin hukumomi. Shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta Yobe, Dr. Muhammad Mamman ya rasu.
Tsohon dan majalisar wakilai, Farouk Lawan, ya yi magana kan halin da ya tsinci kansa a cikin a zaman da ya yi a gidan yari. Ya bayyana cewa ya koyi darussa sosai.
Tsohon ministan wasanni kuma shugaban kungiyar MEN, Solomon Dalung ya yi kiran da aka saki DCP Abba Kyari. Ya bayyana cewa ci gaba da tsare shi ba adalci ba ne.
Gwamnatin tarayyar Najeriya ta nuna rashin jin dadinta kan yajin aikin kungiyar ASUU. Ta bukaci shugabannin jami'o'i su rike albashin mambobin kungiyar.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari