Manyan Labarai A Yau
Rundunar 'yan sandan jihar Kaduna ta fito ta yi magana kan wasu rahotannin da ke cewa 'yan bindiga sun sace mutane sama da 100 yayin da suke ibada a coci.
Sanannen malamin addinin Musulunci a jihar Kano, Sheikh Malam Aminu Daurawa, ya yi magana kan kisan ta'addancin da aka yi wa matar aure da yaranta a Kano.
'Ya bindiga dauke da makamai sun kai hare-hare a wasu coci guda uku a jihar Kaduna. 'Yan bindigan sun yi awon gaba da mutane da dama yayi hare-haren.
A ranar Lahadi, 18 ga watan Janairun 2026 aka kammala buga gasar cin kofin nahiyar Afrika (AFCON) a Morocco. Akwai kasashen da suka fi lashe kofin a tarihi.
Tsohon karamin Ministan ilmi a gwamnatin marigayi Muhammadu Buhari, Emeka Nwajiuba, ya ayyana shirinsa na yin takarar shugaban kasa karkashin ADC a 2027.
Rundunar sojojin Najeriya ta fito ta yi martani kan wasu rahotanni masu cewa dakarunta na shirin yin bore saboda karancin albashi. Ta bayyana yadda lamarin yake.
Rahotanni sun nuna cewa kananan yan kwangila da suka fito zanga zanga a Abuja sun toshe ma'aikatar kudi, sun hana karamar minista, Doris Uzoka-Anite shiga ofis.
Wani jirgin sama na kamfanin Qatar Airways ya yi saukar gaggawa jim kadan bayan tashinsa a filin jirgin kasa da kasa a Legas, babu wanda ya ji rauni.
Kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN), ta yi alhinin rasuwar malamin addinin Musulunci, Imam Abubakar Abdullahi, wanda ya ceci Kiristoci lokacin rikicin Plateau.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari