Manyan Labarai A Yau
Gwamnan jihar Gombe, Inuwa Yahaya, ya sallami shugaban hukumar ilmin bai daya ta jihar (SUBEB) daga kan mukaminsa. Gwamnan ya nada sabon shugaba.
Wasu jami'an sojoji sun shiga hannu bayan an zarge su da yunkurin gudanar da juyin mulki a kasar Guinea-Bissau. Hakan na zuwa ne ana shirin fara kamfen na zabe.
Wasu 'yan bindiga dauke da makamai sun kai harin ta'addanci a jihar Kebbi. 'Yan bindigan sun yi garkuwa da mataimakin shugaban majalisar dokokin jihar.
Babbar jam'iyyar adawa ta kasa watau PDP ta bayyana cewa ba za ta fasa babban taronta na kasa da ta shirya a Ibadan ba duk da hukuncin babbar kotun tarayya.
Babbar Kotun Tarayya mai zama a Abuja ta umarci jam'iyyar PDP ta dakatar da shirinta na yin babban taronta a Ibadan, babban birnin jihar Oyo a watan Gobe.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya nada Gwamna AbdulRahman AbdulArazaq a matsayin shugaban kwamitin aiwatar da shirin raya gundumomi watau RHWDP.
Wasu tsagerun 'yan bindiga dauke da makamai sun kai harin ta'addanci a jihar Sokoto. 'Yan bindigan sun kashe wani basarake tare da wasu mutane a yayin harin.
Wata jarida ta kara tattaro bayanai kan sojoji 16 da ake zargin hukumomi sun tsare su ne bisa zargin hannu a shirin juyin mulkin da bai yi nasara ba.
Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya gargadi kan sulhun da ake yi da 'yan bindiga. Gwamnan ya ce sulhun yana kawai jinkirta rikici ne ba magance shi ba.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari